Yadda Ronaldo Ya Burge Magoya Baya A Wasansa Na Farko A Man United

 


Cristiano Ronaldo ya haska filin wasa na Old Trafford, bayan da ya saka kwallaye 2  ragar New Castle, a wasan farko da ya buga bayan da ya yi wa Manchester United kome.

Ronaldo ne ya ci kwallaye 2 a cikin 4 da Manchester United ta zura wa New castle a wasan da aka tashi 4-1.

Cikakkiyar sa’a guda bayan alkalin wasa Anthony Taylor ya busa usur din tashi wasa, magoya baya sun yi ta hayaniya da ba ya misaltuwa

Daruruwan magoya bayan sun zabi kada su bar filin wasan har sai kungiyar ta karbi bukatarsu ta neman Ronaldo ya gana da tashar talabijin.

Bayan Ronaldo ya amsa wannan kira ne aka ci gaba da sowa ta murna da jinjina gad an wasan.

Yanzu kwallaye 120 ne Ronaldo ya ci wa Manchester United, wanda ya ci kwallayensa na farko tun bayan da ya bar kungiyar  shekaru 12 da suka wuce zuwa Real Madrid, kwallayen da suka dora United din a saman teburin gasar Firimiyar Ingila.

Ronaldo ya ci kwallaye 118 a wasanni 292 da ya buga wa Manchester united daga shekarar 2003 zuwa 2009, lokacin da ya koma Real madrid a kan kudi Fam miliyan 80.

A cikin shekaru 12, ya ci kwallaye 551 a real Madrid da Juventus, kafin ya yin a Unikted kome mai ban mamaki a kan kudi fam miliyan 12.8.


Post a Comment

0 Comments