‘Yan Bindiga A Nijeriya Sun Yi Garkuwa Da Wani Hakimi A Neja

 


Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta tabbatar da sace Mahmud Aliyu, Hakimin Wawa a karamar hukumar Borgu ta jihar da ake zargin ‘yan bindiga ne da aikatawa.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata hira da Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN) a Minna.

Jami’in ya ce, an yi garkuwa da Hakimin ne a daren Asabar da misalin karfe 10 na dare a fadarsa, sai dai tuni ‘yan sanda sun fara bin sawun‘ yan bindigar don ceto hakimin kamar yadda majiyarmu ta tabbatar.

 


Post a Comment

0 Comments