Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

'Yan Bindiga Sun Arce Bayan Sun Yi Artabu Da Mutanen Shinkafi

  ‘Yan bindiga da safiyar jiya Juma’a sun sake kai hari Karamar hukumar Shinkafi dake Jihar Zamfara, inda suka yi artabu da mutanen garin, k...

 


‘Yan bindiga da safiyar jiya Juma’a sun sake kai hari Karamar hukumar Shinkafi dake Jihar Zamfara, inda suka yi artabu da mutanen garin, kafin daga bisani a tura jami’an tsaro.

Rahotanni sun ce ‘yan bindigar dake karkashin wani da ake kira Kachalla Turji sun kai harin ne domin tursasawa mutanen Shinkafi kin amincewa da sabbin dokokin da Gwamna Bello Matawalle ya saka domin dakile hare haren da ake samu a fadin jihar.

Daya daga cikin shugabannin garin Suleiman Shuaibu Shinkafi ya shaidawa RFI Hausa cewar an yi artabu sosai tsakanin mazauna Shinkafi da ‘Yan bindigar kafin zuwan tawagar sojoji da ‘Yan sanda abin da ya sa barayin suka gaggauta janyewa daga garin.

Shinkafi ya ce mazauna garin sun yi nasarar kashe daya daga cikin ‘Yan bindigar kafin janyewar su, yayin da suma suka harbi mazaunin garin guda.

Jihar Zamfara na ci gaba da fuskantar hare haren ’Yan bindiga dake sace shannu da mutane, tare da hallaka jama’a ba tare da kaukautawa ba.

Ko a Talatar nan ‘Yan bindigar sun sace dalibai maza da mata sama da 70 a Kayan Maradun lokacin da suke rubuta jarabawa, kasa da mako guda bayan sakin daliban kwalejin aikin gona dake Bakura.

Wannan ya sa Gwamna Matawalle rufe daukacin makarantun jihar da hana cin kasuwannin mako-mako da saka dokar hana fitar dare da kuma hana sayar da man fetur da yawa ga jama’a, matakin da ya girgiza ‘Yan bindigar.


No comments