‘Yan bindiga sun hallaka mutum akalla 34 tare da raunata wasu da dama a wani hari da suka kai a kauyen Madamai da ke karamar hukumar Kaura...
‘Yan bindiga sun hallaka mutum
akalla 34 tare da raunata wasu da dama a wani hari da suka kai a kauyen Madamai
da ke karamar hukumar Kaura a Kudancin jahar Kaduna.
Daruruwa sun tsere daga gidajensu
bayan wani harin 'yan bindiga da ya janyo asarar rayuka akalla 34, maharan sun
kona gidaje bayan kashe-kashen jama'a a kauyen Madamai da ke karamar hukumar
Kaura na yankin kudancin jahar Kadunan.
Mista Samuel Aruwan wanda shi ne
Kwamishinan harkokin cikin gida da tsaron Jihar ta Kaduna ya tabbatar da
aukuwar harin a wata sanarwar da ya fitar a yau din nan.
An soma tuhumar wasu da ake zargin
nada hannu a harin inji Aruwan, har wa yau a jiya Lahadin, wasu 'yan bindiga
sun kai hari kan masu ibada a wani coci da ke Kachia a jahar ta Kaduna inda
suka kashe mutum guda da raunata wasu da dama.
Rahotanni na cewa jama'a na tserewa
saboda fargabar ramuwar gayya, sai dai an jibge jami'an tsaro a yayin da
gwamnan jihar Nasiru El-Rufai, ya umurci Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar,
da ta gaggauta kai ma wadanda harin ya rutsa da su kayayyakin agaji.
Daruruwan Jama'a ne yanzu haka ke
gudun hijira a yankin Kudancin Kaduna sakamakon karuwar hare-haren 'yan bindiga
da rigingimun masu nasaba da addinai tare da kabilanci
No comments