Wasu 'yan bindiga sun kashe jami'an tsaron Nijeriya 12 a wani hari da suka kai karshen makon da ya gabata kan wani sansanin soji...
Wasu
'yan bindiga sun kashe jami'an tsaron Nijeriya 12 a wani hari da suka kai
karshen makon da ya gabata kan wani sansanin soji a jihar Zamfara da ke arewa
maso yammacin kasar, kana suka sace makamai da kona gine -gine, in ji majiyoyin
tsaro.
Ba a
dai bayyana ko su wanene suka kai samamen na ranar Asabar a Mutumji ba, amma
sojoji na ci gaba da luguden wuta kan 'yan fashin daji wadanda ake zargi da
laifin garkuwa da mutane.
An
kuma katse hanyoyin sadarwa a Zamfara da wasu sassan makwabciyar jihar Katsina
a kokarin hana yan fashin sakat.
Wata
majiya ta shaida wa kamfanin dillacin labaran Faransa AFP cewa “Maharan sun
kutsa cikin sansanin ne da misalin karfe 10:30 na safe kuma suka fafata da
sojojin a wani mummunan artabu,” in ji wata majiyar tsaro.
"Sun
fatattaki sojojin sun kashe 12 daga cikinsu. da suka hadar da sojojin ruwa
tara, da soja da 'yan sanda biyu."
Sansanin
da ke Mutumji, gundumar Dansadau, mai tazarar kilomita 80 daga Gusau babban
birnin jihar, muhimmin wuri ne da sojojin kasar ke amfani da shi wajen shirya
dabaru da tattara bayanai a yakin da suke yi da yan bindiga a jihar.
Zuwa
yanzu dai rundunar sojin Nijeriya bata ce komai dangane da batun ba tukunna.
-BBC Hausa
No comments