Marigayi Sanusi Bala Daga Wakilinmu MADOGARA ta labarto cewa; ‘yan bindiga a jihar Zamfara sun kashe wani mutum mai suna Sanusi Bala Shi...
![]() |
Marigayi Sanusi Bala |
Daga Wakilinmu
MADOGARA
ta labarto cewa; ‘yan bindiga a jihar Zamfara sun kashe wani mutum mai suna
Sanusi Bala Shinkafi. Lamarin ya faru ne a yau Laraba, a inda ‘yan bindigar
suka yi masa kisan gilla a titin Shinkafi zuwa Kaura Namoda.
Falalu Hassan, ya wallafa cewa; “Innalillahi wa’inna Ilaihi Raji'un. Yanzu haka ina Sokoto nake samun labarin bakin ciki na kashe dan uwanmu Sanusi Bala Shinkafi. ‘Yan bindiga ne suka kashe shi a hanyar Shinkafi zuwa Kaura Namoda. Shi babban Yaya ne ga abokina, Alhaji Ahmad Bala Maths, shugaban Kamfanin Mass communication Nigeria Enterprises”, ya tabbatar.
Ya
kara da cewa; “Marigayi Sanusi Bala ba
kawai dan uwa bane, Uba ne da dukkanin ma’ana. Allah ya jikansa da Rahama ya
karbi shahadarsa, ya isar mana ga jininsa da aka shekar bisa zalunci”, inji shi.
Kazalika
shima dan uwan Marigayin ya tabbatar da kashe dan uwan na shi a shafinsa na
Facebook, inda ya labarta cewa; “Innalillahi wa’inna Ilaihi Raji'un. ‘Yan
bindiga sun kashe dan uwana Sanusi Bala Shinkafi a titin Moriki. Muna rokon
Allah ya karbi shahadar shi ya gafarta masa kurakurensa. Wallahi mun yi rashin
Uba garkuwan gidanmu Sadauki”, ya nusasshe.
Jihar
Zamfara dai na daya daga cikin jihohin Arewa maso yamma da ‘yan bindiga suka
addabe ta da kashe-kashe da kuma garkuwa da jama’a. Wanda wannan dalilin ya
sanya gwamnatin jihar ta dauke matakin katse hanyoyin sadarwa baki daya.
No comments