Rahotannni daga jihar Sokoto a arewa maso yammacin Nijeriya na cewa a kalla mutum ashirin ne suka mutu kana wasu da dama suka jikkata saka...
Rahotannni daga jihar Sokoto a arewa maso yammacin Nijeriya na cewa a kalla mutum ashirin ne suka mutu kana wasu da dama suka jikkata sakamakon wani hari da 'yan bindiga suka kai garin Gatawa cikin karamar hukumar Sabon Birni.
Shaidu sun ce maharan sun kuma cinna wa rumbuna hatsi wuta tare da sace kayan abinci masu dimbin yawa.
Wannan harin dai na zuwa sa'o'i ashirin da hudu da 'yan bindigar suka aukawa garin Gangara mai makwaftaka.
Wani matashi da aka sace wa 'yar uwa, ya ce maharan sun yi harbe-harben kan mai uwa da wabi, abin da ya sa mutane suka yi ta-kai-ta-kai.
Sannan ya ce sun kona dammunan hatsi masu dumbin yawa. Mutumin ya kara da cewa akasarin al'ummar garin sun tsere. Sai dai ya ce ba su san adadin wadanda suka mutu ba, kasancewar mutane sun tarwatse don tsira da rayukansu.
"Duk ga mu nan mun yi gudun hijira, mazanmu da mata da yara. Wasu sun gudu Nijar wasu sun tafi garuruwa da ke makwabtaka. Wasu sun samu guiduwa da dabbobinsu.
"An tafi da kanwar babana, garin ya yamutse, abinci ma ba mu da shi."
Ita ma wata matar da ta tsallake da kyar zuwa Sokoto ta shaida min ta waya cewa 'yan bindigar sun tafi da diyarta.
"Mu mata muna cikin gida sai dai idan mun ji harbe-harbe muke samun gduuwa. Muna cikin gida kawai sai ga su sun shigo gida, muka samu muka tsere, amma cikin wadanda suka kwasa har da 'ya'yana," in ji ta.
Honorabul Sa'idu Maino Ibrahim dan majalisar jiha mai wakiltar Sabon Birni Ta Kudu, ya ce 'yan bindiga sun addabi yankin a'amarin da ya jefa al'umma cikin halin kaka-na-ka-yi.
"Sun tafi da kusan mutum 30 sannan sun harbe sama da 20 wadanda har yanzu mun kasa zuwa kwashe gawarwakinsu balle a binne. A garin Gangara ne abin ke faruwa.
"Duk da cewa babu hanyar sadarwar muna samun bayanai ne daga wadanda suka gudu zuwa jamhuriyyar Nijar, su ne suke kira su gaya mana.
"Sannan yanzu haka ga wasu a gidana suna samun mafaka cikin wadanda suka gudo din. Wasu kuma sun gudu Sabon Birni."
BBC ta yi kokarin tuntubar kakakin rundunar 'yan sandan jihar Sokoto ASP Sanusi Abubakar amma haka ba ta cimma ruwa ba.
Al'amarin satar mutane don neman kudin fansa na ci gaba da ta'azzara, a'amarin da ya sa Majalisar Dattawan Najeriya ta bukaci Shugaba Muhammadu Buhari ya ayyana 'yan fashin dajin da suka addabi yankin arewacin kasar a matsayin 'yan ta'adda, tare da ayyana yaki a kansu.
No comments