Daga Ammar Muhammad ‘Yan bindiga sun kashe soja daya tare da garkuwa da wata matar aure da ‘ya’yanta biyu a Unguwar Milgoma dake kus...
Daga Ammar
Muhammad
‘Yan bindiga sun kashe soja daya tare da
garkuwa da wata matar aure da ‘ya’yanta biyu a Unguwar Milgoma dake kusa da
Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello dake Shika a Zariya ta jihar Kaduna.
Wakilinmu ya
labarto mana cewa lamarin ya auku ne da misalin karfe 9 na daren ranar Litinin
kamar yadda mazauna Unguwar suka tabbatar mana.
Majiyarmu ta labarta
mana cewa sojan da ‘yan bindiga suka raunata bayan sun yi musayar wuta a tsakaninsu
a lokacin da sojojin suka yi yunkurin dakile harin ‘yan bindiga ya cika ne a
wani asibiti da ba a bayyana sunansa ba ya zuwa hada rahoton nan.
Majiyarmu ta
labarta mana cewa ‘yan bindigar sun zo da yawan gaske da adadin ya kusan kai wa
40 dauke da muggan makamai inda suka yi harbin kan mai uwa da wabi bayan da
suka farmaki al’ummar Unguwar.
Sai dai gamayyar
Jami’an tsaron sa kai na KADVIS (Kaduna State Vigilance Service) da sojoji da ‘yan
sanda sun yi hanzarin kawo wa Unguwar dauki bayan da suka amsa kiran gaggawa da
aka yi musu, inda majiyarmu ta ce bayan da ‘yan bindigar suka lura da isowar
Hukumomin tsaron ne suka bude musu wuta inda a nan ne suka yi musayar wuta da
ya yi sanadin rasuwar soja daya.
Babu tabbataccen
rahoto kan ko an jikkata ‘yan bindiga ya zuwa hada rahoton nan.
Malam Haruna
Shika, wani mazaunin Unguwar, ya shaidawa Daily Trust cewa hukumomin tsaro sun
yi nasarar kwato yara shida da aka yi garkuwa da su a Kasuwan [a’a a Zariya.
Laftanar Joy
Abah, Mukaddashiyar Daraktan hulda da
jama’a na sojoji na Barikin sojoji na Depot Zariya ta ce ba a tabbatar mata da
mutuwar sojan ba tukunna ya zuwa hada rahoton nan.
No comments