Kwamishiniyar Ma'aikatar Jinkai, Hajiya Faika Ahmad Daga Hussaini Ibrahim, Gusau Gwamnatin jihar Zamfara karkashin jagorancin Gwamna...
![]() |
Kwamishiniyar Ma'aikatar Jinkai, Hajiya Faika Ahmad |
Daga Hussaini Ibrahim, Gusau
Gwamnatin jihar Zamfara karkashin
jagorancin Gwamna Bello Muhammad Matawalle ta maida 'yan gudun Hijira 450 garuruwan su sakamakon harin 'yan ta'adda.
Kwamishiniyar Ma'aikatar Jinkai,
Hajiya Faika Ahmad ce ta bayyana haka a lokacin da ake kwashe ‘yan gudun Hijira da ke Zaune a cikin garin
Gusau, babban birnin jihar.
Hajiya Faika Ahmad ta bayyana cewa, wadannan
‘yan gudun Hijira daga Kananan hukumomin
Kauran Namoda, Zurmi, Shinkafi, Birnin Magani da Gusau, an maida su garuruwan
su ta hannun Sarakuna iyayen kasa tare da rakiyar jami'an tsaro. “kuma mun bai
wa ‘yan gudun Hijira tallafin kayan masarufi da kudi da zai ba su damar zama a cikin
garuruwan na s”, inji Kwamishiniyar.
Kuma ta tabbatar da cewa, Ma'aikatar
ta na iyaka kokarin ta wajen tallafawa mata da kananan Yara da suka rasa abinci
da muhalli domin ganin sun samu saukin rayuwa.
Kuma Gwamnati jihar, karkashin
jagorancin gwamna Matawalle tare da Gwamnatin tarayya na iyaka kokarinsu su wajrn
ganin sun tallafawa al'umma da annoba ta shafa a fadin jihar ta Zamfara.
No comments