Wani bincike da kungiyar SERAP dake sanya ido akan tattalin arziki da kuma tabbatar da jagoranci na gaskiya a Najeriya ta fitar yace aka...
Wani bincike da kungiyar SERAP dake
sanya ido akan tattalin arziki da kuma tabbatar da jagoranci na gaskiya a
Najeriya ta fitar yace akalla Yan Najeriya miliyan 27 da rabi ne basa iya samun
naira dubu 100 a shekara guda.
Rahotan da kungiyar ta gabatar a
Lagos yace wannan adadin da ya kai kusan kashi 49 na al’ummar kasar kuma ya
dada fito da tsananin talaucin da ya addabi jama’ar Najeriya duk da arzikin
Allah Ya wadata kasar da shi.
Rahotan da aka yiwa lakabi da ‘Yadda
cin hanci da rashawa suka yiwa harkar bada ilimi da kula da lafiya da samar da
ruwan sha illa’, ya mayar da hankali ne a shiyoyi 6 na Najeriya domin sanin
halin da jama’a suke ciki.
Yayin gabatar da rahotan, Elijah
Okebukola, wani babban mai bincike a Cibiyar horar da jami’an yaki da cin hanci
da rashawa a Najeriya dake karkashin Hukumar ICPC yace kashi 28 na Yan Najeriya
ko kuma mutane miliyan 15 da rabi ke rayuwa tsakanin naira dubu 200 zuwa kasa
da dubu 100 a shekara, yayin da kashi kusan 11 ke samun tsakanin naira dubu 201
a shekara zuwa naira dubu 300, sai kuma kashi 12 da rabi dake samun sama da
naira dubu 300 a shekara.
Rahotan yace akasarin wadanda suka
fi jin radadin halin kuncin talaucin da ya addabi jama’ar kasar talakawa ne
wadanda ake ci da gumin su ta irin makudan kudaden da ake warewa domin kula da
lafiyar su da samarwa ‘yayan su ilimi da kuma tsaftacaccen ruwan sha.
Rahotan yace jihohin Najeriya basu
da wata shaidar bayanan dake nuna yadda suke taimakawa jama’a wajen yaki da
talauci a hukumance, ko kuma inganta rayuwar su ta bangaren kula da lafiyar su
da kuma samar musu da ilimi.
Okebukola yace koda an samu
daidaikun jihohin dake kokarin kamanta irin wadannan ayyuka mutanen su basu ma
san ana yi ba.
Rahotan yace daga cikin kashi 79 na
mutanen Najeriya dake zama cikin talauci sama da miliyan 44 sun dogara ne da
shan ruwan rijiya ko kuma rijiyar birtsatsai, yayin da kashi 34 ko kuma miliyan
19 basu damu da zuwa asibitocin gwamnati domin samun magani ba.
Rahotan yace sama da kashi 5 ko
mutane kusan miliyan 3 da suka je asibitin gwamnati an hana su magunguna ko
kuma kular da ta dace.
Rahotan ya kara da cewar sama da
kashi 4 ko kuma mutane miliyan 2 da rabi basu taba samun abinda ake kira
tallafin da gwamnati ke ikrarin rabawa marasa galihu ba.
Kungiyar SERAP tace duk da
tabarbarewar harkar bada ilimi a Najeriya wajen rashin kayan aiki da kuma gine
ginen azuzuwa, talakawa na tunanin samun ingantaccen ilimi a makarantun
gwamnati.
Jaridar Premium Times tace rahotan
ya bukaci sake fasalin kundin tsarin mulkin Najeriya da ake amfani da shi yanzu
domin sanya ‘yancin jama’a na samun ilimi da kula da lafiyar su da kuma
tsaftacaccen ruwan sha a matsayin hakkokin jama’ar kasa.
No comments