‘Yan sanda a Jigawa sun cafke wani mutum dan shekara 35, Abdulmumini Abdullahi, bisa zargin sa da daba wa matarsa mai shekaru 25 wuka ...
‘Yan sanda a Jigawa sun cafke wani
mutum dan shekara 35, Abdulmumini Abdullahi, bisa zargin sa da daba wa matarsa
mai shekaru 25 wuka inda ya kashe ta har lahira a karamar hukumar Babura da
ke jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, ASP Lawan Shiisu, shi ne ya tabbatar da kamun wanda ake zargi a wata sanarwa da ya fitar a garin Dutse a ranar Laraba.
Shiisu ya ce an cafke wanda ake zargin ne bayan da ‘yan sanda suka samu rahoto a ranar 2 ga watan Satumba cewa ya yi kwanton bauna inda ya kashe matarsa, Sahura Sule a kan hanyar daji.
Ya bayyana cewa, bayan samun labarin ne, ‘yan sanda suka ziyarci wurin da lamarin ya faru inda suka dauki Marigayiyar zuwa Babban Asibitin da ke Babura.
Ya ya bayanin cewa Marigayiyar tana da shaidar sukar wuka a ciki da gwiwar hannunta na dama, kuma likita a asibitin ya tabbatar da mutuwar ta.
Inda ya ce an mika gawarta daga bisani ga ‘yan’uwanta domin su yi mata sutura su bizne ta.
Shiisu ya kara da cewa an mika
shari’ar zuwa sashen binciken manyan laifuka na jihar a hedikwatar ‘yan sanda
da ke Dutse, domin ci gaba da bincike.
No comments