Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

‘Yan Sanda Sun Sha Alwashin Kamo Wadanda Suka Kashe Akunyili

  Kwamishinan ‘yan sandan Anambra, Mista Tony Olofu, ya sha alwashin cewa rundunar, tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro, za su kamo ...

 


Kwamishinan ‘yan sandan Anambra, Mista Tony Olofu, ya sha alwashin cewa rundunar, tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro, za su kamo wadanda suka kashe Dr Chike Akunyili.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ba da rahoton cewa Dr Akunyili, wanda wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka kashe, shi ne mijin Marigayi Darakta Janar na Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC), Mrs. Dora Akunyili.

Kwamishinan ‘yan sandan, wanda ya yi magana yayin tabbatar da mutuwar Akunyili, ya nemi a kwantar da hankali sannan ya jaddada cewa za a tona asirin wadanda suka aikata laifin kuma “za a yi maganin su ”.

Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan (PPRO), DSP Tochukwu Ikenga, ya fitar a ranar Laraba a Awka ta ce Olofu ya ziyarci inda aka kashe Akunyili a NKpor da wasu wurare biyu da aka aikata miyagun laifuka.

Ikenga ya nakalto Olofu yana cewa ‘yan bindigar sun rasa duk wata ‘yan adamtaka da sanin yakamata.

Sanarwar ta ce da misalin karfe 5 na yamma a kusa da Nkpor Roundabout kuma ba tare da wani tsokana ba, wasu ‘yan bindiga suka kai hari suka harbi wani Sifeton ‘yan sanda wanda ke da alaƙa da Mutum Mai Muhimmanci.

No comments