-Abdulaziz Ganduje ya kai karar mahaifiyarsa Gwaggo EFCC kan batun almundahana. Babban dan Gwamnan Kano, Abdulaziz Ganduje ya maka mahai...
-Abdulaziz Ganduje ya kai karar mahaifiyarsa Gwaggo EFCC kan batun almundahana.
Babban dan Gwamnan Kano, Abdulaziz Ganduje ya maka
mahaifiyarsa Hafsat Ganduje gaban hukumar yaki da yiwa tattalin arziki zagon
kasa ta EFCC akan zargin da yake yi mata da almundahana da kuma azurta kanta ta
hanyoyin da ba su dace ba.
Tuni hukumar EFCC ta aikewa da Hafsat Ganduje mai dakin
Gwamnan Kano da goron gayyata domin amsa tambayoyi kan zargin amma ta ki amsa
gayyata, ba kuma tare da ta bayar da wani uzuri a rubuce ba.
A cikin wasikar da Abdulaziz Ganduje ya aikewa da EFCC ta
shafi badakalar filaye da kuma kudade.
Sai dai kakakin hukumar EFCC Wilson Uwujaren yaki cewa komai game da batun da
aka yi masa tambaya akai.
Idan ba a manta ba, a baya an zargi Gwamnan Kano Alhaji
Abdullahi Umar Ganduje da yin badakala ta sama da dalar Amurka miliyan biyar, inda
aka nuno shi a wani faifan bidiyo yana karbar dalar Amurka daga cikin kudaden
'yan kwangila, Gwamnan dai ya karyata bidiyon tare da kai karar jaridar Daily
Nigerian da mawallafinta Jaafar Jaafar gaban kotu game da batun bidiyon Dala.
-Daily Nigerian Hausa
No comments