YANZU-YANZU: Jami'an Kwastam Sun Budewa Kwamishina Wuta A Katsina

 
Rahotannin da MADOGARA ke samu a gaggauce na nuni da cewa; jami'an Hukumar Kwastam ta Nijeriya sun budewa Kwamishinan Kananan Hukumomi da Harkokin Masarautu ta jihar Katsina wuta a hanyarsa ta Daura zuwa Katsina. 

Lamarin ya faru da safiyar yau Talata a daidai garin Mai Aduwa daga Daura.  

Kwamishinan, Alhaji Ya'u Umar Gwajo Gwajo shi ne wanda Jami'an Kwastam din suka budewa tawagarsa wuta, sai dai babu labarin asarar rai ko raunata wani daga tawagar Kwamishinan.

Cikakken bayani na nan tafe.


Post a Comment

0 Comments