Sarkin Bungudu ta jihar Zamfara, Hassan Attahiru ‘Yan bindiga dauke da muggan makamai sun kai wa tawagar Sarkin Bungudu, Hassan Attahiru h...
![]() |
Sarkin Bungudu ta jihar Zamfara, Hassan Attahiru |
‘Yan bindiga dauke da muggan makamai sun kai wa tawagar Sarkin Bungudu, Hassan Attahiru hari a titin Abuja zuwa Kaduna.
Hassan Attahiru Sarkin Gargajiya ne a jihar Zamfara.
Majiyarmu ta shaidawa MADOGARA cewa duk da Jami’an tsaron da ke raka tawagar Sarkin, hakan bai hana su sace Sarkin ba bayan da suka budewa tawagarsa wuta wanda hakan ya ba su nasarar tarwatsa tawagarsa.
Wani ganau ya shaida mana cewa lamarin ya faru ne da yammacin yau Talata a daidai Dutse gaban Kamfanin Olam kilomita kadan kafin a iso kwaryar cikin garin Kaduna.
Ya zuwa yanzu babu wani karin bayani dangane da harin. Sai dai wakilinmu da lamarin ya rutsa da shi ya dauki bidiyon yadda harin 'yan bindigar ya rutsa da masu ababen hawa da yawa a hanyarsu ta zuwa.
Zamu wallafa bidiyon daga bisani.
No comments