YANZU-YANZU: Shugaban NIS Babandede Ya Yi Ritaya, Isah Jere Ya Karɓi Ragama
Labarin da muka samu da ɗimi-ɗiminsa daga LEADERSHIP HAUSA ya tabbatar da cewa shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta Nijeriya, CGI Muhammad Babandede ya yi ritaya da maraicen Juma’ar nan.

Tuni har ya damƙa ragama ga Babban Matamakinsa Isah Idris Jere da misalin ƙarfe biyar na yammacin nan.

Bayan sauyin shugabancin dai, manyan mahukuntan hukumar sun shiga wata ganawar sirri tare da sabon shugaban hukumar da kuma mai ritaya.

Babandede dai ya shafe tsawon shekara biyar yana shugabantar hukumar ta NIS.

Za mu kawo muku ƙarin bayani nan gaba

Post a Comment

0 Comments