Cristiano
Ronaldo yana cikin 'yan wasan Manchester United da za ta kara da Young Boys
ranar Talata a Champions League.
United
za ta ziyarci Young Boys domin buga wasan farko a cikin rukuni a gasar
Champions League ta bana.
Sai
dai kungiyar ba za ta je wasan da Edison Cavani, sakamakon jinya da yake yi,
wanda bai buga mata wasan Premier League ranar Asabar ba.
0 Comments