Hukumar kula da yanayi ta Nijeriya ta yi gargadin samun rushewar gine-gine da hadarurruka a titunan kasar sakamakon ambaliya, ya...
Hukumar kula da yanayi ta Nijeriya ta yi gargadin samun rushewar gine-gine da hadarurruka a titunan kasar sakamakon ambaliya, yayin da ake ci gaba da zabga ruwan sama a fadin kasar.
Hukumar ta shawarci ƴan Nijeriya su yi shirin ko ta kwana, don kiyaye ɓarnar da hakan ka iya haifarwa.
Sakamakon hasashen da ta yi na baya bayan nan, hukumar ta yi gargadi a kan santsin hanyoyi, da samun ƙaƙarfar iska mai kaɗawa.
Haka kuma ta ce akwai yiwuwar ambaliyar za ta shaifi su kansu hanyoyi da tituna, ta kuma janyo rushewar gadojin da jama'a ke amfani da su kamar yadda majiyarmu ta labarto mana.
No comments