Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Abu Hudu Da PDP Ta Cimma A Taronta Na Kasa

  Kwamitin zartarwar jam'iyyar PDP na kasa ya amince da matakin da kwamitin raba mukamai a jam'iyyar ya yi na keÉ“ewa yankin arewacin...

 


Kwamitin zartarwar jam'iyyar PDP na kasa ya amince da matakin da kwamitin raba mukamai a jam'iyyar ya yi na keɓewa yankin arewacin ƙasar kujerar shugaban jam'iyyar al'amarin da ya haifar da tada jijiyoyin wuya.

Haka kuma kwamitin yayin zaman da ya yi yau Alhamis a Abuja, ya amince a yi musayar mukaman jam'iyyar PDP wato na kudu su koma arewa, na arewa kuma su koma kudu.

Da farko dai an yi zaton za a kai ruwa rana kan matakin, amma sai ga shi 'ya'yan babbar jam'iyyar adawar sun tashi lami lafiya.

Sanata Ibrahim Tsauri shi ne sakataren jam'iyyar na kasa kuma ya shaidawa BBC cewa muhimman abubuwa hudu taron nasu ya cimma a yau.

Shugaban Jami'iyya zai fito daga arewa

Za a yi musaya mukamai tsakanin 'yan kudu da arewa

Matsayar bai shafi mukamin wani É—an takara ba a yanzu

Kowannen mutum na da hakkin takara

Sanata Tsauri ya ce tsarin da ke kudin tsarin mulki su ke bi kuma sun amince da hakan ne domin tabbatar da wanzuwar dimokuradiyya.

Sannan ya ce PDP ta saba da rigingimu cikin gida amma suna shiga daki suke dinke kansu, kuma a yanzu an kawo karshen maganar ko dambarwasu.

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya ce matakin da PDP ta dauka kan yankin da zai fitar da ɗan takara da sauran batutuwa su za su yanke hukuinci kan zaɓen 2023.

Takaddama kafin taron

Kafin taron nasu na yau Alhamis takaddama ta kaure a jam'iyyar bayan kwamitin raba muƙaman ya keɓe wa arewacin Najeriya kujerar shugaban jam'iyya, alamar da ke nuna cewa bangaren kudu ne zai fitar da dan takarar shugaban kasa a zaben 2023.

Sakataren jam'iyyar PDP na kasa, Sanata Ibrahim Tsauri, ya shaida wa BBC cewa, "Kwamitin zartarwa ne daman ya kafa wannan sabon kwamitin, kuma ya gama aikin shi, don haka zai dawo wa kwamitin zartarwa abin da ya samu, a duba abin da aka yi da nazari a amince ko a yi gyare-gyare ko ma ƙin amincewa da shi, daga nan sai a san abin da ake ciki".

Kwamitin raba mukaman, wanda gwamnan jihar Enugu, Ifeanyi Ugwuanyi, ke jagoranta ya ba da shawarar a yi juyin-waina ko rawar 'yan mata tsakanin kudu da arewa.

Kenan za a keɓe kujerar shugabancin jam'iyyar ga yankin arewacin kasar, yayin da kwamitin ya ce sai kwamitin zartarwar jam'iyyar ne zai yanke hukunci a kan yankin da za a ba wa takarar shugaban kasa.

Fusata wasu jiga-jigan

Tuni dai kebe wa arewacin Najeriya kujerar shugaban jam'iyyar ya fusata wadansu jiga-jigana - yayin da wasu ke ganin an yi hakan ne da kyakkyawar manufa, wadansu kuma na zargin ana so a yi wa arewa dodo-rido, kuma ba za ta saɓu ba.

Amma tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya ce sun zuba wa kwamitin zartarwar ido.

Ya kara da cewa: "Zaben da aka yi na shekara shida da suka gabata, PDP ba ta da wani kwarjini a arewacin Najeriya, don haka idan an yi ne domin a dawowa da jam'iyyar PDP kwarjini da farin jini to babu laifi, amma idan ana dauko maganar dole sai dan wata shiyya ne zai fito takarar shugaban kasa to wannan kam ba za ta sabu ba."

Wani abin da ya rura wutar takaddamar shi ne matakin da gwamnonin kudancin Najeriyar suka dauka cewa lallai sai shugabancin kasar ya koma yankin su a zaben 2023.

Jam'iyyar PDPn dai ta yi ta kakkaucewa maganar a baya, amma 'yan magana kan ce ranar wanka ba a boyon cibi, saboda haka wannan taron kowanne yanki zai san matsayinsa.

Wannan ne ma ya sa masana siyasa, irin su Farfesa Kamilu Sani Fagge, na jami'ar Bayero ta Kano ke cewa sai jam'iyyar ta yi taka-tsantsan, saboda komai na iya faruwa.

Ya ce, "Wannan taro da jam'iyyar PDP za ta yi a nan ne kashin bayan dorewarta a matsayin jam'iyya ko kuma wargajewa, ko da ba ta mutu ba zai kawo mata rigingimu.

"Kuma tuni jam'iyyar ta dauki mataki, saboda a tsarinsu in da shugaban jam'iyya ya fito, ba nan ne dan takarar shugaban kasa ya ke fitowa ba.

"Saboda jam'iyyar ta nuna za ta bai wa arewa shugabancin ta,to ba ma sai an fada cewa ga daga in da dan takarar shugaban kasa zai fito ba. Don haka ko da wasu sun zauna a cikin jam'iyyar to za su yi mata kafar angulu ne kawai."

Wannan tsari na raba mukamai a tsakanin yankuna da shiyyoyi dai tamkar wani siradi ne wanda dolen jam'iyyar PDPn sai ta ratsa ta tsallake, kasancewar a karshen wannan watan ne jam'iyyar za ta yi babban taron ta na kasa, inda magoya bayan na ta za su zabi sabbin shugabanni.


-Rahoton BBC 

No comments