Wata babbar kotun tarayya a birnin Tarayya Abuja ta yanke wa Faisal, ɗan Abdulrasheed Maina, tsohon shugaban hukumar sauye-sauye ta fansho...
Wata babbar kotun tarayya a birnin Tarayya Abuja ta yanke wa Faisal, ɗan Abdulrasheed Maina, tsohon shugaban hukumar sauye-sauye ta fansho hukuncin ɗaurin shekara 24 a gidan yari, kamar yadda gidan talabijin na NTA ya ruwaito.
A yayin yanke hukuncin a ranar Alhamis, Mai Shari'a Okon Abang ya samu Faisal da laifuka uku da suka haɗa da halatta kuɗin haram, wanda hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa ta'annati EFCC ta tuhume shi da su.
Mai Shari'a Abang ya ce EFCC ta gabatar da hujjojin da ke tabbatar da cewa Faisal ya yi amfani da wani asusun ajiya na banki na jabu a bankin UBA, inda ta can ne mahaifinsa Maina ya yi zambar kudi har naira miliyan 58.1.
Kotun ta ce an tura kuɗin ne asusun mai ɗauke da sunan Alhaji Faisal Farm 2, kuma Faisal da mahaifinsa sun cire kuɗaɗen daga tsakanin Oktoban 2013 zuwa Yunin 2019.
Faisal bai halarci zaman kotun ba, ana zargin ya tsere daga ƙasar tun tuni.
Mai shari'ar ya yanke masa hukuncin ɗaurin shekara 14 ne kan laifuka biyu sai kuma shekara goma kan laifuka biyu.
An yanke wa Faisal hukuncin shekara 24 ne amma zai yi zaman gidan kaso na shekara 14 ne saboda zai yi zaman shekarun ne a lokaci guda.
A watan Fabrairun 2021 ne Hukumar EFCC ta ce Faisal ya tsere Amurka.
A zaman kotun da aka yi a lokacin ne lauyan EFCC, Mohammed Abubakar, ya bayyana wa Justice Okon Abang hakan.
Lauya Mohammed Abubakar ya ce daga bayanan da suka samu Faisal ya tsere Amurkar ne ta jamhuriyar Nijar.
Sai dai a lokacin kotun ta bayar da belin Faisal kan kudi naira miliyan 60 da mai tsaya masa wanda dole ya kasance dan majalisar wakilai kamar yadda rahoton BBC ya tabbatar.
No comments