Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince a soma biyan daliban da ke karanta fanin koyarwa a jami'o'in gwamnati naira 75,000 a kowa...
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince a soma biyan daliban da ke karanta fanin koyarwa a jami'o'in gwamnati naira 75,000 a kowanne zangon karatu na digiri.
Sannan za a ke biyan ɗaliban da ke karatun NCE a kwalajen koyarwa ta tarayya naira 50,000 a kowanne zangon karatu.
Ministan Ilimi, Mallam Adamu Adamu ne ya sanar da hakan a Abuja lokacin bikin ranar malamai da aka gudanar jiya Talata.
Wannan wani bangare ne na sake karfafawa dalibai gwiwa musamman masu karatun fanin koyarwa a jami'i'o da kwaleji da ke fadin Najeriya.
No comments