Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Dauke Layukan Sadarwa: Khalifan Tijjaniya Ya Yi Kira Ga Gwamna Masari

Khalifa Ali Saidu Alti (da jan kyalle a wuya) a yayin jawabi a jan taron Mauludin.  Daga Hussaini Yero Sakamakon mawuyacin hali ...

Khalifa Ali Saidu Alti (da jan kyalle a wuya) a yayin jawabi a jan taron Mauludin. 

Daga Hussaini Yero

Sakamakon mawuyacin hali da al'ummar yankunan da aka dauke layukan Sadarwa a wasu yankuna na jihar Katsina, Khalifan Tijjaniya, Ali Sa'idu Alti Funtuwa, ya yi kira ga Gwamna Aminu Masari da a sassauta domin al'umma na cikin mawuyacin hali.

Khalifa Ali Saidu Alti ya bayyana hakan ne a wajen taron Mauludi da ya gudana a Zawiyyar Sheka Abubakar Alti da ke Bakori Road Funtua cikin jihar Katsina.

Khalifa ya kara da cewa, Gwamnatin Jihar Katsina Karkashin jagorancin gwamna Masari da jami'an tsaro suna iyaka kokarin su wajen yaki da 'yan ta'adda da suka addabi al'ummar jihar Katsina; "kuma a kodayaushe muna yi masu addu'a domin ganin sun samu nasara", inji Khalifan Tijjaniya.

"Duk da wannan masifa mu maka jawo da hannayenmu sakamakon munanan ayyuka da muke aikatawa da Allah ya hana sun zamo ruwan dare. Masu karfi ba su taimakon raunana, masu arziki ba su taimakon marayu da marasa karfi, kowa kansa da iyalansa ya sani. Shugabanni ba su yin abin da ya dace, an kauce ma tafarkin tsarin Allah don haka Allah ya jarrabe mu da masifu kala-kala", a cewarsa. 

A kan haka Khalifan Tijjaniya Ali Saidu Alti ya yi kira ga Gwamna Aminu Masari da Shugabanin tsaro da su taimaka wajen dawo da layukan Sadarwa domin yana taimakawa wajen tona asirin 'yan Bindiga idan suka shigo gari wajen shaidawa jami'an tsaro domin kai ma al'umma dauki; "rashin sadarwa yana kara ba 'yan Bindiga damar cin karen su babu babbaka a cikin karkara wanda yanzu haka suna afkawa garuruwan", ya tabbatar. 

No comments