Wasu ‘yan Najeriya kalilan da aka bayyana da masu kumbar susa na sace gangar danyen man fetur, miliyan 42.25 a duk shekara wanda...
Wasu ‘yan Najeriya kalilan da aka bayyana da masu kumbar susa na sace gangar danyen man fetur, miliyan 42.25 a duk shekara wanda darajarta ya kai Dala Biliyan 3.6.
Shugaban kamfanin mai na kasa, Mele Kolo Kyari ne ya bayyana haka a wajan wani taro da aka yi a Abuja.
Kyari yace wasu manyan mutanene a Najeriya ke yin wannan aika-aika inda kuma ya kara da cewa, banda asarar kudaden, akwai kuma wasu kudaden da suke kashewa wajan gyaran bututun man da ake fasawa.
No comments