Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Faransa Za Ta Taimaka Wa Najeriya Wajen Magance Matsalar Tsaro

  RFI ta labarto cewa; shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ya yi alkawarin zurfafa zumunci tsakanin kasarsa da Najeriya, musamman ma ta wajen...

 


RFI ta labarto cewa; shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ya yi alkawarin zurfafa zumunci tsakanin kasarsa da Najeriya, musamman ma ta wajen tinkarar matsalar tsaro.

Hakan na kunshe ne a wata sanarwar da Macron din ya aike wa shugaba Muhammadu Buhari, ta ofishin jakadancin Faransa a Najeriya,  don taya shi murnar tunawa da cikar kasar shekaru 61 da samun yancin kai.

A cikin sanarwar Macron ya jaddada kudirinsa na yaukaka zumunci tsakanin Faransa da Najeriya, wanda zai kai ga habakar tattalin arziki da bunkasar al’umma.

Shugaban na Faransa ya ce tun bayan da ya ziyarci kasar a shekarar 2018, dangantaka tsakanin Najeriya da Faransa na ci gaba da habaka, musamman ma a fannin tattalin arziki.

No comments