Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnan Jihar Kaduna Zai Rushe Kimanin Gidaje Dubu 10 A Zariya

Fatima Idris Zariya A yau Lahadi 3 ga watan Oktoban 2021 ne gwamnatin jihar Kaduna karkashin Gwamna Malam Nasiru Ahmed El-Rufai ...



Fatima Idris Zariya

A yau Lahadi 3 ga watan Oktoban 2021 ne gwamnatin jihar Kaduna karkashin Gwamna Malam Nasiru Ahmed El-Rufai ta turo dubban jami'an tsaro da motocin rushe gini a wata Anguwa dake makwabtaka da Kwalejin koyon tukin jirgin sama dake Zariya (NCAT) domin rushe Anguwar da ake zargin su da mallakar filayen ba tare da ka'idar mallakar fili ba.

Unguwar ta Graceland tana karamar Hukumar Sabon Garin Zariya ne ta jihar Kaduna. 

Wakiliyarmu ta ziyarci Anguwar don jin ra'ayin jama'ar Anguwar. 

Honorabul Gunji Makama shi ne mai Anguwar wani sashe a Anguwar ya tabbatar da cewa matakin da Gwamna zai daukarwa Anguwar Graceland ya sabawa dokar kasa.

Mai Anguwar ya tabbatar da cewa mafi yawan gidajen dake wannan Anguwar suna da takardunsu.

Honorabul ya kara cewa ko a lokutan baya hukumar kula da tsara birane ta jihar sun je domin daukar mataki mai kama da hakan amma sai al'ummar Anguwar suka garzaya kotu don daidaita al'amarin.

Ya zuwa yanzu tuni gwamnatin jihar ta turo motocin rushe gini tare da gamayyar jami'an tsaro masu yawan gaske.

Bincike ya tabbatar da cewa akalla mutane sama da dubu dari biyu ne za su rasa gidajensu idan har rusau din ya tabbata a yau.

No comments