Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Gwamnatin Jihar Kaduna ta Karasa Rushe Makabarta Da Makarantar 'Yan Shi'a a Zariya

Daga Wakilinmu Jaridar Africa Daily News ta labarto cewa; Hukumar tsara birane ta Jihar Kaduna wanda aka fi sani da KASUPDA kar...


Daga Wakilinmu

Jaridar Africa Daily News ta labarto cewa; Hukumar tsara birane ta Jihar Kaduna wanda aka fi sani da KASUPDA karkashin Jagorancin Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru El-rufa'i ta kammala rushe makabarta hade da makaranta mallakin Mabiya Mazhabin Shi'a Almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky a babban Dodo dake birnin Zariya, lamarin da har cikin daren Alhamis ana ta ce-ce-ku-ce akan batun a fadin Jihar.

An rushe muhallin ne da yammacin ranar Alhamis inda hukumar tsara biranen suka hallara a muhallin dauke da kayan aiki tare da rakiyar jami'an tsaro inda suka rushe ajujuwan karatun tare da ribde wurin baki daya daga ciki harda kaburbura.

        Hoton kaburburan da aka rubde.

Lamarin dai ya jawo mutane suna ta Allah-wadai bisa abin da ya faru, inda suka bayyana cewar wurin ba a kan hanya bane kuma "an gina shi bisa ka'ida amma duk da hakan bai hana Gwamnan rusawa ba", inji su.

Wani daga cikin mazauna yankin da ya nemi a sakaye sunansa ya yi  ma wakilinmu karin bayani akan faruwar lamarin inda ya bayyana cewar Gwamnan "ya yi hakan ne saboda borin kunya ganin kotu ta saki shugaban Harkar Musulunci da aka fi sani da 'yan shi'a, Shaikh Ibraheem Zakzaky".

Shi kuwa Malam Iliyasu Muhammad mazaunin Unguwar Kakaki ya bayyana cewar zalunci ne kawai tuburan yasa aka rusa muhallin domin wurin bai tare hanyar komai ba. 

Tuni dai 'yan Shi'ar dake yankin suka hallara a muhallin domin gane ma idonsu abin da ke faruwa da kuma tattara wasu kayayyakinsu ka da "zauna gari banza su yi awon gaba da su", a cewar su. 

Muhallin Makarantar Fudiyya wacce akwai kaburburar mutum uku a wurin dake Babban Dodo Zariya, dama tuni Gwamnatin jihar Kaduna ta fara rusa shi tun a shekarar 2018 biyo bayan dirar mikiyar da sojojin Nijeriya suka yi akan mabiya Mazhabin Shi'a a Zaria. Sai dai ba fa kammala rusa wurin baki daya ba, sai a wannan karon. 

No comments