Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Harkar Musulunci Ta Ja Kunnen Majalisar Dinkin Duniya Kan Rahoton Tsaro

Harkar Musulunci a Nijeriya ta gargadi sashen Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da sha'anin walwala da samar da tsaro da ke...



Harkar Musulunci a Nijeriya ta gargadi sashen Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da sha'anin walwala da samar da tsaro da ke da mazauni a babban birnin tarayya Abuja dangane da bayani maras tushe da ta fitar a ranar 5/10/2021 ga ma'aikatanta musamman da kuma daukacin al'umma a kan gagarumar Muzaharar kwanaki bakwai a jere da aka tsara gudanarwar, lamarin da ba gaskiya ba ne kuma ba a aiwatar da shi ba.

Wannan bayani ya bayyana ne ga 'yan Jarida ta hannun Shugaban Dandalin Yada Labarai na Harkar Musulunci a Nijeriya, Malam Ibrahim Musa, a Takardar Sanarwar Manema Labarai wadda ya rattaba wa hannu, ya kuma fitar da ita a ranar Talatar da ta shige.

Sanarwar Manema labaran ta bayyana cewa, "Muna so mu bayyana karara da babbar murya cewam Harkar Musulunci a Nijeriya karkkshin Jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ba ta da wani kuduri na gudanar da Muzaharar kwanaki bakwai a jere, wadda ya kamata a fara gudanarwa a cikin makon da ya gabata! Kuma rashin ganin wanzuwar gudanar da Muzaharar ya nuna gaskiyar cewa lamari ne kawai na sawwalawar wadanda suka kirkiri rahoton na kanzon kurege."

Harkar ta Musulunci a Nijeriya ta kuma yi kira ga Majalisar ta Dinkin Duniya da cewa, ta rinka tuntubar ta a nan gaba, a duk lokacin da ta samu wani rahoton sha'anin tsaro dangane da al'amarin Harkar ta Musulunci a Nijeriya, domin kaucewa shirga karya da kuma faduwa babu nauyi a idon duniya. "Abin kunya ne a ce wannan bayani na karya da kazafi ya fito ne daga sashin kula da walwala da sha'anin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya. Idan da a ce ba ita ta fitar da irin wadannan bayanai ba, to da lallai ta yiwu ba za mu mayar da hankali wajen yin martani ba, saboda mun san cewa irin wannan rahoto yana samo asali ne daga Jami'an tsaro wadanda suka dukufa wajen durkusar da kasar nan, wadda 'yan kasarta ke cikin kangin talauci da sunan kwantar da tarzoma ko dakile hadari. Muna fata nan gaba idan irin wannan shirgegiyar karya ta isa zuwa ga ofishin Majalisar Dinkin Duniya, to ya zama ta tuntubi Harkar Musulunci a Nijeriya domin samun gaskiyar lamari," in ji Sanarwar Manema labaran.

Daga karshe Harkar ta Musulunci a Nijeriya ta yi tuni tare da karin haske ga Majalisar ta Dinkin Duniya a kan cewa, gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta tauye wa Jagoranta, Shaikh Ibraheem Zakzaky da mai dakinsa Malama Zeenah Ibrahim 'yancinsu na fita kasar waje domin neman lafiyarsu. Ta kuma bukaci Majalisar ta Dinkin Duniya da ta dauki matakin da ya dace dangane da wannan lamari. 

"Za mu so mu yi amfani da wannan dama wajen yin kira ga al'ummatan kasa da kasa da su matsa lamba ga gwamnatin Muhammadu Buhari wadda ta aiwatar da kisan Kiyashin Zariya da ta gaggauta sakin Fasfo din Shaikh Ibraheem Zakzaky da mai dakinsa Malama Zeenah Ibrahim, domin su iya samun damar fita kasar waje domin samun cikakkiyar kulawar Likitoci irin wadda ta dace da su da kuma yanayin halin rashin lafiyar da suke fama da ita tun da dai babbar Kotun Tarayya da ke Abuja da babbar Kotun Jihar Kaduna dukkanin su sun wanke tare da tabbatarwa da duniya cewa ba su aikata wani laifi ba. Babu wani Shugaban kasa a tarayyar Nijeriya wanda ya yi tafiye-tafiye zuwa kasar waje neman lafiya kamar Shugaban kasa Muhammadu Buhari, to saboda haka me ya sanya yake hana sauran 'yan kasa 'yancin da suke da shi na fita kasar waje domin samun cikakkiyar kulawar Likitoci?" In ji sanarwar Manema labaran.

Abin da ke kasa cikakken bayani ne wanda takardar sanarwar Manema labaran ta kunsa:

Majalisar Dinkin Duniya ta yi taka-tsantsan kan rahoton tsaro na karya  kan Harkar Musulunci a Nijeriya

Harkar Musulunci a Nijeriya ta lura da wani rahoton shawara da sashen kula da walwala da sha'anin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya (UNDSS) da ke Abuja Nijeriya/sashen Afirika/DRO, wanda babu kunya babu tsoron Allah ya yi zargin cewa Harkar Musulunci a Nijeriya za ta gudanar da Muzaharar kwanaki bakwai a jere a cikin birnin Abuja, wadda za ta fara gudana a ranar shida ga wannan wata na Oktoba da muke ciki a matsayin Muzaharar Allah wadai dangane da kisan kare dangi da aka yi a 'yan kwanakin nan a yayin Tattakin Yaumul Arba'een. Abin mamaki sai ga shi wannan rahoto ya samu lambar yabo ta A1 dangane da sahihancin majiyar da aka samo bayanin da kuma ingancin bayanin ga Majalisar ta Dinkin Duniya.

Muna so mu bayyana karara da babbar murya cewa, Harkar Musulunci a Nijeriya karkashin jagorancin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) ba ta da wani kuduri na gudanar da Muzaharar tsawon kwanaki bakwai a jere, wanda ya kamata a fara gudanarwa a cikin makon da ya gabata! Kuma rashin ganin wanzuwar gudanar da Muzaharar ya nuna gaskiyar cewa lamari ne kawai na sawwalawar wadanda suka kirkiri rahoton na kanzon kurege.

Maimakon bugewa da wannan kamfe na karya da kazafi daga wannan sashen Ma'aikata na Kungiyar Majalisar Dinkin Duniya, Sakatare Janar na Majalisar ta Dinkin Duniya ya kamata ne ya bukaci gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta mika gawar mutum bakwai, 'yan’uwa Musulmi mabiya Mazhabar Shi'a fararen hula, wadanda ba su dauke da makami, wadanda gamayyar jami'an tsaro Sojoji da 'yan Sanda suka kashe haka siddan a yayin gudanar da Tattakin Yaumul Arba'een da ya gudana a cikin watan da ya gabata, domin danginsu su yi masu jana'iza, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. Tattakin Yaumul Arba'een lamari ne da ake gudanarwa a duk shekara cikin tsari da lumana domin tunawa da cika kwanaki Arba'in da aiwatar da kisan gilla ga Imam Husain (A.S), jikan Manzon Allah, Annabin Rahma, Annabi Muhammad (SAWA).

Abin mamaki ne a ce Hukumar duniya kamar Majalisar Dinkin Duniya a ce an rude ta da rahoton bogi na karya, a yayin kuma da a gefe guda ba ta yi komai ba dangane da batun kisan gilla da aka yi wa mutum 347, lamarin da jami'an tsaro Sojojin tarayyar Nijeriya suka aikata wanda ya saba wa duk wata doka da ka'ida tare kuma da binne gawawwakin wadanda suka kashe a asirce a cikin kabari na bai-daya a shekarar 2015, kamar yadda gwamnatin jihar Kaduna karkashin Gwamna Nasiru Elrufa'i ta tabbatar.

Hakazalika Majalisar Dinkin Duniya ba ta ce uffan dangane da bacewar daruruwan mutane ba tun bayan kisan Kiyashin Zariya, wanda aka kaddamar kimanin shekaru shida ke nan da suka gabata, ballantana kuma ta ce wani abu dangane kan batun mutane sama da sittin (60+) da ake tsare da su a gidan Yarin Kuje tun cikin watan Yuni na shekarar 2019, wadanda suke dauke da raunukan harbin bindiga da aka yi masu, wadanda aka kama su bayan kammala Muzaharar kiran a saki Shaikh Zakzaky a cikin garin Abuja.

Abin kunya ne a ce wannan bayani na karya da kazafi ya fito ne daga sashin kula da walwala da sha'anin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya. Idan da a ce ba ita ta fitar da wadannan bayanai ba, to da lallai ta yiwu ba za mu mayar da hankali wajen yin martani ba, saboda mun san cewa irin wannan rahoto yana samo asali ne daga Jami'an tsaro wadanda suka dukufa wajen durkusar da kasar nan, wadda 'yan kasarta ke cikin kangin talauci da sunan kwantar da tarzoma ko dakile hadari. Muna fata nan gaba idan irin wannan shirgegiyar karya ta isa zuwa ga ofishin Majalisar Dinkin Duniya, to ya zama ta tuntubi Harkar Musulunci a Nijeriya domin samun gaskiyar lamari.

Za mu so mu yi amfani da wannan dama wajen yin kira ga al'ummatan kasa da kasa da su matsa lamba ga gwamnatin Muhammadu Buhari wadda ta aiwatar da kisan Kiyashin Zariya da ta gaggauta sakin Fasfo din Shaikh Ibraheem Zakzaky da mai dakinsa, Malama Zeenah Ibrahim, domin su iya samun damar fita kasar waje domin samun cikakkiyar kulawar Likitoci irin wadda ta dace da su da kuma yanayin halin rashin lafiyar da suke fama da ita tunda dai babbar Kotun Tarayya da ke Abuja da babbar Kotun Jihar Kaduna, dukkanin su sun wanke tare da tabbatarwa da duniya cewa ba su aikata wani laifi ba. Babu wani Shugaban kasa a tarayyar Nijeriya wanda ya yi tafiye-tafiye zuwa kasar waje neman lafiya kamar Shugaban kasa Muhammadu Buhari, to saboda haka me ya sanya yake hana sauran 'yan kasa 'yancin da suke da shi na fita kasar waje domin samun cikakkiyar kulawar Likitoci?

SA HANNU:
IBRAHIM MUSA
SHUGABAN DANDALIN SADARWA NA HARKAR MUSULUNCI A NIJERIYA

No comments