Daga Wakilinmu Hukumar hana fataucin mutane ta kasa (NAPTIP) a ranar Alhamis a Abuja ta hada yara biyu Musulmai wadanda wasu Inyamurai su...
Daga Wakilinmu
Hukumar hana fataucin mutane ta kasa (NAPTIP) a ranar Alhamis a Abuja ta hada yara biyu Musulmai wadanda wasu Inyamurai suka sace su a Lafia ta jihar Nasarawa suka kuma sauya musu suna daga sunan Musulunci zuwa na Inyamurai. Sai dai hukumar ta NAPTIP ta yi nasarar kwato su tare da hada su da iyayensu.
Yaran sune Sheriff Umar da Abdullahi Adamu, masu shekaru uku kowannensu kuma suna zaune tare da iyayensu a wata Unguwa a Lafia lokacin da wani makwabcinsu ya sace su a watan Mayu.
Da take jawabi yayin taron mika yaran, Darakta Janar na NAPTIP, Misis Fatimah Waziri-Azi, ta lurantar da cewa yaran biyu sun fito ne daga yara 47 da aka bayar da rahoton cewa an sace su a fadin jihar Nasarawa.
A cewarta, NAPTIP ta samu wasu bayanai cewa yara 47 da aka dauka daga Lafia a jihar Nasarawa an sayar da su ga mutane daban-daban a jihar Anambra.
“Mun samu bayanai daga hukumar tsaro ta farin kaya nan take muka shiga cikin aiki kuma jami’ai daga sashen ayyukanmu da bincike sun sami nasarar bin sawun wasu da ake zargi tare da cafke su.
“Kama wadanda ake zargi ya kai ga ceto Sheriff da Abdullahi, yara kanana ne, Sheriff da Abdullahi sune sunayen haihuwarsu amma lokacin da aka yi safarar su, an ba su sunayen Ibo.
“An bai wa daya sunan Chigomezu Njoku ɗayan kuma an ba Chibueze Daniel. Wannan nasara ya samu ne ta hanyar taimakon hukumomin ‘yan’uwanmu masu aiwatar da doka,’ yan sanda, DSS, NSCDC, “in ji Waziri-Azi.
“Mun ji cewa yana da mahimmanci mu sake hada yaran nan da iyayensu, babu bukatar mu rike su tare da kara hana iyayensu da suka cire rai daga ganin yaran nasu, ” in ji ta.
Waziri-Azi ta ce za a gurfanar da wadanda ake zargi zuwa kotu yayin da hukumar za ta bibiyi lamarin domin tabbatar da an yi adalci.
Ta ci gaba da cewa hukumar za ta bi diddigin lamarin da kuma kudaden da ke cikin ayyukan, ta kara da cewa kamun wadanda ake zargi zai kawo rukushi ga masu garkuwa da mutanen.
No comments