Daga Abbakar Aleeyu Anache Hukumomin Nijar sun tabbatar da mutuwar jami'an tsaron kasar 11, bayan wani harin kwantan bauna da aka kai ...
Daga Abbakar Aleeyu Anache
Hukumomin Nijar sun tabbatar da mutuwar jami'an tsaron kasar 11, bayan wani harin kwantan bauna da aka kai kan ayarin motocin kwantoman Bankilare dake yankin Tillaberi kusa da iyakar kasar da Burkina Faso a ranar Laraba.
Adadin da ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ta sanar ranar juma'a ya zarce wadanda jami'an yankin suka ruwaito tun farko.
Harin da wasu da ake zargin mayaka masu ikirarin jihadi ne suka kai kan ayarin da ke rakiyar kwantomar shi ne na farko da aka kaiwa jami'an gwamnati a Tillaberi.
Yankin dake kan iyaka uku, tsakanin Nijar Burkina Faso da Mali, yayi kaurin suna da manyan hare-hare daga masu ikirarin jihadi da ke da alaka to Al'Qaeda da Kungiyar IS.
No comments