Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da ƙudurin kasafin kuɗin shekarar 2022 a gaban zaman haɗin gwiwa na 'yan majalisun tarayyar ...
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da ƙudurin kasafin kuɗin shekarar 2022 a gaban zaman haɗin gwiwa na 'yan majalisun tarayyar ƙasar.
Shugaban ya ce kasafin na shekarar 2022, zai mayar da hankali ne wajen kammala ayyukan da gwamnatinsa ta soma kuma ƙudurin kasafin kuɗin na 2022, wanda ya kai naira tirliyan 16 da ɗigo 39.
Kuɗin dai, ƙari ne a kan naira tiriliyan 13.98 na kasafin kuɗin shekara 2021.
Gwamnatin shugaban kasar ta bayyana shirinta na ciyo karin bashi don samun karin kudi har Naira tiliyan 6 da biliyan 258, da zata cike gibin da za a samu a kasafin kudin da shugaban zai gabatar na shekarar 2022.
Daga cikin kudin da shugaban kasar ya gabatar a kasafin kudin na 2022, har da muhimman bangarorin da za a warewa kudade kamar hukumar zaben kasar, wadda ake sa ran tanadar mata karin naira biliyan 100, don shirin kasar na tunkarar babban zaben 2023.
A yayin gabatar da kasafin kudin dai, shugaban na Najeriya ya sanar da ajiye gangar man fetir daya a kan farashin dala 57, da kuma hako man fetir ganga kusan miliyan biyu a kullum.
Sai kuma canjin dala daya a kan Naira 410 da silai 15, da kuma hasashen samun kudin shiga Naira tiriliyan 3 da digo 15 daga bangaren man fetur.
'Za mu amince da kasafin a cikin wannan shekarar'
Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan |
Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ahmad Lawan ya ce majalisar dokoki za ta amince da kasafin kudin 2022 kafin karshen wannan shekarar.
Lawan ya bayyana haka ne a jawabinsa na maraba kafin shugaba Buhari ya gabatar da kasafin kudin 2022 a zauren majalisar dokokin kasar.
Bayan godewa shugaban kasa Muhammadu Buhari, shugaban majalisar dattawan ya ce 'yan majalisar za su yi aiki tukuru domin ganin an soma aiki da sabon kasafin kudin a cikin sabuwar shekara.
No comments