Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Korona ta kashe fiye da mutum dubu 700 a Amurka

  Jami’ar Johns Hopkins ta Amurka da ke tattara alƙalumman cutar korona a duniya, ta ce adadin waɗanda cutar Korona ta yi ajali daga lokacin...

 


Jami’ar Johns Hopkins ta Amurka da ke tattara alƙalumman cutar korona a duniya, ta ce adadin waɗanda cutar Korona ta yi ajali daga lokacin ɓarkewarta kawo yanzu a ƙasar ya haura dubu 700.

Wannan adadi shi ne baki ɗayan yawan mazauna birnin Washington, kuma shi ne mafi yawa da wata ƙasa ta fuskanta a duniya.

Korona na ƙara yaɗuwa a Amurka musamman sabon nau’in Delta, inda lamarin ya fi kamari a jihohin kudancin kasar.

Bayan kakkausar sukar da aka fuskanta kan yadda gwamnati ta tunkari annobar korona, a yanzu an yi wa kusan rabin Amurkawa cikakkiyar rigakafin korona.

A duniya baki daya, sama da mutum miliyan biyar aka tabbatar da mutuwarsu, sanadiyar cutar korona. Sai dai kwararru a fannin lafiya na cewa adadin ka iya fin haka saboda wadanda ke mutuwa a gida ba tare da an san takamaimai abin da ya yi ajalinsu ba.

No comments