Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Kotu Ta Tsige Sabon Sarkin Sudan Da Aka Naɗa Tun Kafin Ya Kai Ga Shiga Fada

A ranar Talata ne 12 ga watan Oktoba, wata babbar kotu a jihar Neja, ta umarci Mohammed Barau Kontagora da ya daina bayyana kanshi a matsayi...


A ranar Talata ne 12 ga watan Oktoba, wata babbar kotu a jihar Neja, ta umarci Mohammed Barau Kontagora da ya daina bayyana kanshi a matsayin Sarkin Sudan na Kontagora na 7.

Wannan umarni na kotu ya fito biyo bayan ƙorafi da sauran masu neman sarautar mutum 15 suka kai gaban kotun dangane da kujerar.

Rahotanni sun bayyana cewa waɗanda ake ƙarar sun hada da sabon Sarkin, Mohammed Barau Kontagora, Alkalin Alkalai na jihar Neja, da kuma Kwamishinan Ƙananan Hukumomi na jihar.

Alkalin Kotun, Mai Shari’a Abdullahi Mika'ilu, ya dakatar da wanda ake ƙarar Mohammed Barau Kontagora, daga bayyana kanshi a matsayin Sarki na 7, biyo bayan ƙarar da sauran masu neman kujerar suka shigar a ranar 11/10/2021.

“Mun bada umarni na wucin gadi ga waɗanda ake ƙara, wakilansu, dama duk wani mutum koma wanene, daga bayar da ofishi ga wanda ake ƙara a matsayin Sarkin Sudan na 7, biyo bayan ƙarar da wasu daga cikin masu neman kujerar suka shigar a ranar 11/10/2021.” Inji Kotun

Lauyan masu ƙara, W’Y. Mamman Esq. ya roƙi kotu da ta hana Barau bayyana kanshi a matsayin Sarki na 7.

Sauran mutum 15 masu neman Sarautar suna ƙalubalantar yadda aka zaɓi Sarkin, wanda ya mayar da Barau Sarkin Kontagora.

Ya zuwa yanzu dai an ɗaga sauraron ƙarar har zuwa ranar Laraba, 20 ga watan Oktoba.

Barau Kontagora Ya Karɓi Takardar Zama Sarki

Kafin a kai ga zuwa kotu, da kuma umarnin da kotun ta bayar, Barau Kontagora ya karɓi takardar da ta bayyana shi a matsayin sabon Sarkin Sudan.

An bashi takardar a gidan gwamnatin jihar Neja dake babban birnin jihar.

Gwamna Abubakar Sani Bello, wanda ya samu wakilcin Kwamishinan Ƙananan Hukumomi, Emmanuel Umar, ya roƙi Sarkin da ya yi tafiya da kowa, don tabbatar da zaman lafiya a tsakanin al’umma, wanda yace hakan na da matuƙar muhimmanci ga cigaban masarautar.


No comments