Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Kudurin Gwamna Abdullahi Sule Na Bunkasa Ilimin Kimiyya Da Fasaha A Kananan Makarantu Zai Kawo Ci Gaban Tattalin Arzikin Nasarawa, Inji Othman Bala

Daga Zubairu M Lawal Gwamna Abdullah Sule na jihar Nasarawa ya jaddada aniyarsa na bunkasa harkar Ilimin kimiyya da fasaha ga da...


Daga Zubairu M Lawal

Gwamna Abdullah Sule na jihar Nasarawa ya jaddada aniyarsa na bunkasa harkar Ilimin kimiyya da fasaha ga dalibai dake kananan Makarantu a fadin jihar.

Gwamna Abdullah Sule ya ce; ilimin kimiyya da fasaha shi ne ginshikin gina tattalin arzikin kasashe da dama a duniya.

"Duk kasar dake da matasa masu hazaka wajen kirkirar fasaha, kasar na samun ci gaba a fannoni daban-dàban", inji Gwamnan. 

Gwamna Abdullah Sule ya ci gaba da cewa; irin wannan sana'a ta walda tana cikin kimiyya da fasaha. "Kuma tana rike mutum har tsawon rayuwarsa. Saboda lokacin da nake karatu a Amurka da tallafin Gwamnatin ya yanke ba ya shigowa, wannan sana'a da na dogara da ita ta taimaka min a karatuna sosai ".l, ya tabbatar. 

Gwamna Abdullah Sule ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ziyarci makarantar koyon sana'ar hannu da Gwamnatin Jihar ke ginawa a garin Lafia a ranar Talata.

Da yake zantawa da wakilinmu bayan ziyarar Gwamnan, Tsohon Kwamishinan bunkasa matasa da harkan Wasanni ta jihar Nasarawa Alhaji Othman Bala Adam. Ya ce; wannan kudurin na Gwamna Abdullah Sule na bunkasa Ilimin kimiyya da fasaha zai kawo ci gaba sosai a fadin jihar Nasarawa.

Ya ce; wannan kudurin yana da mahimmanci ga dalibai, ya kara da cewa kasashen Dlduniya irin su kasar Chaina, Amurka, Koria da Rasha da sauransu suna gina yara tun daga kananan makarantu da Ilimin kimiyya.

"Ire-iren cajan waya da robobin waya da kayan kwalliya da kayan wasan da na gidaje idan ka je kasashen dalibai ke kerawa", inji shi.

Ya ce; Gwamna Abdullah Sule ya yi alkawarin bunkasa harkar tattalin arzikin jihar Nasarawa. Da samar da ayyukan yi na dogaro da kai, ga matasa maza da mata.

Othman Bala Adam ya yi kira ga iyaye da su karfafa wannan kudurin ta hanyar tura 'ya'yansu zuwa makaranta domin cin gajiyar kudurin Gwamna Abdullah Sule.

Ya kuma kara rokon al'ummar jihar Nasarawa da su bai wa Gwamnatin Jihar goyon baya domin bunkasa ayyukan ci gaba.

No comments