Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

MAAUN Ta Mika Ta'aziyyarta Kan Mutuwar Hannah M. Agwaza Shagba

Hukumar gudanarwa ta Jami’ar Maryam Abacha American University a Nijar ta mika sakon ta’aziyyarta ga Mataimakin Sakataren Ilimi ...Hukumar gudanarwa ta Jami’ar Maryam Abacha American University a Nijar ta mika sakon ta’aziyyarta ga Mataimakin Sakataren Ilimi na Jami’ar, Mista Bemdoo Agwaza kan rasuwar mahaifiyarsa, Mama Hannah Mbawekwagh Agwaza Shagba wacce ta rasu a ranar Larabar 13 ga watan Oktoban 2021 bayan gajeruwar rashin lafiya. .

Sakon ta’aziyyar na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Shugaban MAAUN, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo wanda aka aika wa Mista Bemdoo Agwaza zuwa jiharsa ta Binuwe. Hukumar gudanarwar ta bayyana rasuwar  Hannah Agwaza a matsayin babban rashi ga Ma’aikatan Jami’ar MAAUN, wanda ya hada da manya da kananan ma’aikata, malamai da kuma dalibai baki daya.

“A madadin hukumar gudanarwa na Jami’ar Maryam Abacha American University a Nijar, muna mika ta’aziyyarmu ga iyalan Hannah Agwaza da dukkan al'ummar jihar Binuwe da Najeriya baki daya,” in ji Farfesa Gwarzo.

Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya yi addu'ar Allah Madaukakin Sarki da ya ba mu da iyalinta jurewar rashinta. 

Marigayiya Mama Hannan ta mutu ne a ranar 13/10/2021 tana da shekaru 74. Ta mutu tana da yara 9 ciki har da Mista Bemdoo Agwaza.

No comments