Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

MAAUN: 'Yan Jarida Sun Nemi Masu Hannu Da Shuni Su Yi Koyi Da Farfesa Abubakar Gwarzo

Kungiyar wakilan kafafen watsa labarai ta Jihar Kano ta kungiyar 'yan jarida ta Nijeriya, wato NUJ ta yabawa wanda ya kafa k...Kungiyar wakilan kafafen watsa labarai ta Jihar Kano ta kungiyar 'yan jarida ta Nijeriya, wato NUJ ta yabawa wanda ya kafa kuma Shugaban Jami'ar Maryam Abacha American University, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo bisa kafa Jami’ar a Kano.

Shugaban kungiyar, Ibrahim Garba Shuaibu ya yi wannan yabon ne a lokacin da wani jami'in Jami'ar, Alhaji Aliyu Kakaki ya jagoranci membobin kungiyar suka zagaye Jami'ar a yammacin ranar Talata.

Ya lurantar da cewa kafa Jami'ar Maryam Abacha American University a Kano ba kawai ta kawo ci gaba ta fuskacin gini bane, ta ma haɓbaka ayyukan zamantakewa da tattalin arziƙin jama'a musamman a yankin da Jami'ar take.

Ya ce kafa Jami’ar a Kano zai bunkasa tattalin arziki da kawo ci gaba na musamman a Jihar da ma kasa baki daya.

Ya ce, “Mutanen Kano musamman 'yan kasuwa, za su ci gaba da yaba irin gudummawar da ya bayar wajen bunƙasa tattalin arziƙi da ci gaban garin.

Ya bayyana gamsuwa da yanayin kayayyakin fasahar da aka sanya a Jami'ar.

Shugaban ya yi amfani da wannan damar wajen godewa Farfesa Gwarzo saboda tallafin da ya ke bai wa matasa da talakawa da sauran masu rauni a jihar ta hanyar Gidauniyarsa ta Adamu Abubakar Gwarzo Foundation (AAG).

A bisa haka, ya yi kira ga sauran masu hannu da shuni a jihar da su yi koyi da Farfesa Gwarzo ta hanyar kafa irin wannan Jami'ar domin haɓbaka ilimi a jihar.

An zagaya da membobin kungiyar wasu wurare a cikin Jami'ar da ya hada da ginin Hukumar Gudanarwa, ajujuwan karatu, dakunan gwaje-gwaje, gidajen ma'aikata, dakunan kwanan dalibai da dakin karatu da sauransu.

No comments