Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Majalisar Zamfara Ta Dakatar Da Membobinta Biyu Saboda Alaka Da 'Yan Ta'adda

  Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta dakatar da membobinta guda biyu da ake zargin suna mu’amala da ‘Yan bindigar da suka hana zaman lafiya ...

 


Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta dakatar da membobinta guda biyu da ake zargin suna mu’amala da ‘Yan bindigar da suka hana zaman lafiya a jihar.

‘Yan majalisar sun hada da Yusuf Muhammad Anka dake wakiltar mazabar Anka da Ibrahim Tukur Bakura dake wakiltar mazabar Bakura.

Daraktan hulda da ‘Yan Jaridu na Majalisar Mustapha Jaafaru Kaura ya ce ‘yan Majalisun guda biyu za su kauracewa zaman majalisar na watanni 3 har zuwa lokacin da za a kammala bincike akan su.

Kaura ya ce tuni aka bai wa kwamitin da’a na Majalisar umurnin gudanar da bincike akan su tare da hukumomin tsaron jihar kamar yadda zaman Majalisar ya amince.

‘Dan Majalisa Yusuf Alhassan Kanoma ya gabatar da bukatar daukar mataki akan ‘Yan Majalisun guda biyu wadanda ya ce suna murna lokacin da ‘Yan bindiga suka kama mahaifin shugaban Majalisar Alhaji Mu'azu Abubakar Magarya.

Kanoma ya kuma zargi ‘Yan Majalisun guda biyu da hannu wajen kashe tsohon ‘dan majalisar dake wakiltar Shinkafi Muhammad G. Ahmad wajen tseguntawa 'yan bindiga bayanan tafiyarsa domin hallaka shi.

‘Dan Majalisar dake wakiltar mazabar Birnin Magaji Nura Dahiru Sabon Birni Dan Ali ya goyi bayan kudirin, inda ya ce duk yunkurin da aka yi na kubutar da mahaifin Kakakin Majalisar daga hannun Bello Turji ya ci tura.

Tuni Majalisar ta tube mutanen biyu daga shugabancin kwamitocin ta, yayin da aka fara bincike akan su.

No comments