Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Mata Da Kananan Yara Miliyan Biyu Ne Za Su Halarci Taron Mako A Zamfara

Daga Hussaini Ibrahim, Gusau Hukumar kula da lafiya matakin farko hadin gwuwa da hukumar UNICEF ta shirya taron makon Mata da Ka...


Daga Hussaini Ibrahim, Gusau

Hukumar kula da lafiya matakin farko hadin gwuwa da hukumar UNICEF ta shirya taron makon Mata da Kananan Yara, taron kwana biyar da za'afara daga ranar mai  Litinin 18/10/2021 zuwa ranar Juma'a 22/10/2021,a cikin Kananan hukumomin shahudo da ke cikin Jihar ta Zamfara.

Sakataren zartarwa na hukumar Lafiya matakin farko ,Dakta Samaila Tukur ne ya bayyana haka alokaci  da yake tattaunawa da wakilin mu a Gusau babban birnin jihar Zamfara.

"Dr Samaila Tukur ya bayyana cewa, jihar Zamfara tabi sahun wajan raya makon Mata da Kananan Yara dan fadakar da su yadda zasu tafiyar da rayuwar su dan kaucewa da kamuwa da cututuka da zata kai ga asarar rayukan su.

Kuma ya qara da cewa,wannan taron mata masu juna biyu ne da Yara "Yan kasa da shekaru biyar zasu halarci Taron makon da za'afara a sati Mai zuwa.

Haka kazalikama Dr Samaila Tukur ya Kuma tabbatar da cewa,kungiyoyin bada tallafi bangaren lafiya hadin gwuya da Gwamnatin jihar Zamfara, Qarqashin jagorancin gwamna Bello Matawalle na iyaka kokarin ta wajan ganin ta tallawa yara kanana da mata masu cikin dan ganin rayuwar su ta inganta.

A karshe Dr Samaila Tukur ya yi kira ga mahalarta taron makon da su daure hularci taron na kwana biyar da za'ayi dan ganin sun amfana da fadakarwa da za'ayi masu a ranakun taron.

No comments