Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Minista Sa'adiya Ta Bada Tallafi A Zamfara

Daga Hussaini Ibrahim Ministan Jinkai Hajiya Sa'adiya Umar Shinkafi ta amsa kiran gwamnan Jihar Zamfara,Hon Bello Muhammad M...



Daga Hussaini Ibrahim

Ministan Jinkai Hajiya Sa'adiya Umar Shinkafi ta amsa kiran gwamnan Jihar Zamfara,Hon Bello Muhammad Matawalle bada tallafi ga al'ummar Zamfara sakamakon mawuyacin hali da ake ciki na matsalar "Yan Bindiga.

 Maiba Minista Saadiya Shawara a bangare Siyasa Alhaji Musa Zubairu Nasarawan Mai layi ne ya jagoranci mika tallafi,ga babban Kwamitin raba tallafin wanda Hon Aminu Sani Jaji ke jagoranta.

Alhaji Musa Zubairu,ya bayyana cewa, Minista a kashin kanta ta bada tallafin ,Shikafa,buhu 1850,Wake 1850,sai Katan dari na Mai da Tumatir na gwagwani katan dari da gishiri da dilar Gwanjo ashirin da sauran su.inji Wakilin Ministan.

"Ya kara da cewa, Wannan tallafi da Minista Saadiya ta bada bashi karun farko ba,ta bada irin shi da dama ga al'ummar Jihar Zamfara.

Kuma Minusta akoda yaushe zuciyarta na tare da al'umma Jihar Zamfara,akoda yau idan abun jindadi ya samu al'umma tana tare su da tayasu farin ciki,dan ma na jajantawa ne tana zuwa da kanta ko tayo aiki dan jajantawa al'umma Jihar Zamfara.akan haka ne take jajantawa al'umma halin da muke ciki na matsalar Yan Bindiga.da fatan Allah zai mana.aganinsu da gaggawa.

Anasa Shugaban Kwamitin bada tallafi, Alhaji Aminu Sani Jaji da ya samu wakilcin , Sakataren Kwamitin ,Abu Jafaru Maradun ya,mika godiyar sa ga Minista Saadiya akan amsa kiran gwamnan Matawalle na bata tallafi dan rabawa al'umma da suka shiga mawuyacin a wannan lokaci da muke fama da matsalar Yan Bindiga.

Sakatare Abu Jafaru Maradun yayi kira ga al'ummar Jihar masu mukaman Siyasa da Hannu da shuni akan suyi koyi da Minista Saadiya wajan tallafawa alumma.

Kuma nan bada jimawaba mai girma gwamna Matawalle zai kaddamar da nashi tallafin a matakin Jihar.

No comments