Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

'Muna son mayar da 'yan gudun hijira zama masu dogaro da kansu'

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Najeriya ta kaddamar da wani shiri na musamman, don samar da abinci da sauran ababen mo...Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Najeriya ta kaddamar da wani shiri na musamman, don samar da abinci da sauran ababen more rayuwa ga 'yan gudun hijira da kuma matan jami'an tsaron da suka mutu a filin daga.

Kwamishinar hukumar, Hajiya Imaan Sulaiman Ibrahim, ta shaida wa BBC cewa, sun bullo da shirin na kawar da yunwa mai taken 'Zero Hunger' a turance, don rage wa wadannan iyalai radadin kuncin rayuwa da suka samu kansu a ciki.

Kwamishinar ta ce akwai bukatar daukacin al'umma su rika taimaka wa gwamnati wurin inganta rayuwar wadannan rukuni na 'yan kasa, lura da cewa hannu daya baya daukar jinka.

"Muna so mu hada hannu da mutane da gwamnatocin jihohi da ma kungiyoyi masu zaman kansu domin tabbatar da cewa kowa ya ba da tasa gudunmuwar wajen inganta rayuwar irin wadannan mutanen."

Hajiya Imaan Sulaiman Ibrahim, ta ce makasudin wannan shiri, shi ne a kawar da yunwa, domin idan aka kawar da yunwa to za a iya amfani da kudin hukumarsu wajen sake wa 'yan gudun hijirar matsugunai.

Ta ce, baya ga samar da matsugunni ga'yan gudun hijrar, za kuma a samar da makarantu a cikin sansanin 'yan gudun hijrar don karatun 'ya'yansu.

Kwamishinar ta ce, "Muna kuma samar da ayyukan yi ga matasa 'yan gudun hjira, domin wasu daga cikinsu sun wuce karatun sakandire, don haka sai mu koyar da su sana'oin dogaro da kai".

Ta ce, daya daga cikin burin hukumarsu, shi ne mayar da matan sojojin da suka rasa ransu a fagen daga masu dogaro da kansu.

Ta kara da cewa: "Haka su ma sauran 'yan gudun hijirar mun fi so mu ga mun mayar da su masu dogaro da kai, ta yadda suma a gaba za su iya taimaka wa na kasa da su," in ji kwamishinar.

Dubban ƴan gudun hijira a Najeriya na cikin halin yunwa babu wajen kwana mai kyau babu magunguna mai kyau.

Najeriya dai na cikin ƙasashen da suke fama da mutanen da rikici ya raba da gidajensu, musamman ma jihar Borno wadda mahukunta suka ce fiye da mutum miliyan ɗaya ne rikicin Boko Haram ya ɗaiɗaita.

-Rahoton BBC HAUSA

No comments