Dan Bala Jarida Radio ta labarto cewa; Musulman Najeriya sun mamaye shafin Facebook na Dr. Ahmad Gumi, shahararren mai fafutukar kare ha...
Dan Bala
Jarida Radio ta labarto cewa; Musulman Najeriya sun mamaye
shafin Facebook na Dr. Ahmad Gumi, shahararren mai fafutukar kare hakkin ‘yan
fashin daji bayan yayi suka ga maulidi a shafin a daidai lokacin da musulman
suke tunawa da ranar haihuwar Annabi
Muhammad SAWA.
A kowace shekara a cikin watan Rabi’ul Awwal, Musulmin
duniya suna tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad ta hanyar karanta
AlÆ™ur’ani mai girma, Æ™asidun yabo ya Annabi da karanta tarihin rayuwar sa.
Shafin Dr. Gumi na Facebook ya samu sharhi sama da 600 har
zuwa lokacin nan a tare da cewa suka yayi akan maulidin, amma da yawan su suna
rubuta "Happy Maulud," duk da
sun karanta sukar da yayi.
Karantarwar Dr Gumi tana fuskantar tsaiko da rashin tasiri
akan mutane bayan ya karkatar da hankalin sa daga taimakon waÉ—anda rikicin yan
fashin daji ya rutsa da su a arewa maso yammacin Najeriya zuwa neman haƙƙin
masu aikata laifin.
No comments