Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

NCC Ta Hana Sayar Da Layukan Waya Ga Wadanda Shekarunsu Bai Kai 18 Ba

  Hukumar sadarwa ta NCC a Najeriya ta hana yi wa 'yan Æ™asar da shekarunsu bai kai 18 ba rajistan layukan waya. A wani rahoto da ta wall...

 


Hukumar sadarwa ta NCC a Najeriya ta hana yi wa 'yan ƙasar da shekarunsu bai kai 18 ba rajistan layukan waya.

A wani rahoto da ta wallafa hukumar NCC ta ce sai mutumin da ya kai 18 kawai za a rinka yiwa rajistan layuka.

NCC ta ce wannan mataki nata ya yi daidai da dokokin mallakar layin waya sashi na 70 na kudin bayanan sadarwar Najeriya na 2003.

A lokacin gabatar da wannan tsari gaban masu ruwa da tsaki da kamfanonin sadarwa ciki harda MTN, kamfanin ya bukaci a rage waÉ—annan shekaru.

MTN ya bukaci NCC ta tsayar da shekara 14 a matsayin mafi kakantar shekarun mallakar layin waya.

Sai dai NCC ta dage akan cewa dole sai mutum ya kai shekara 18 kafin ya mallaki layin waya harda rajista a Najeriya.

No comments