Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Ronaldo Ya Kafa Wani Sabon Tarihi A Kwallon Kafa

  Dan wasan gaba na Portugal Cristiano Ronaldo y akafa wani sabon tarihi a kwallon kafa wajen zama 'dan wasa guda da ya jefa kwallaye gu...

 


Dan wasan gaba na Portugal Cristiano Ronaldo y akafa wani sabon tarihi a kwallon kafa wajen zama 'dan wasa guda da ya jefa kwallaye guda 3 a wasa guda ga kasar sa har sau 10.

Wannan ya biyo bayan nasarar da kasar Portugal ta samu na zazzagawa Luxembourg kwallaye 5 a karawar da suka yi a gasar neman zuwa cin kofin duniya, wadda suka tashi da ci 5-0.

Cristiano Ronaldo ya jefa kwalle 3 shi kadai a karawar, yayin da Bruno Harnendez da Alves Palhenha Gonclaves suka jefa sauran kwallaye guda biyu.

Wannan nasara ta baiwa Ronaldo damar ci gaba da zama dan wasan da yafi kowa zirarar kwallaye a duniya da kwallo 115, yayin da shi kuma ya kafa wani sabon tarihi a matsayin ‘dan wasan da ya jefa kwallaye 3 a raga a wasa guda har sau 10 ga kasar sa.

Yanzu haka Portugal na sahun gaba wajen samun tikitin zuwa gasar cin kofin duniya da zai gudana a Qatar a shekara mai zuwa.

Ita ma kasar Denmark ta zama kasa ta biyu a duniya da ta samu tikitin zuwa gasar cin kofin duniyar da za’ayi a shekara mai zuwa a Qatar, bayan Jamus da ta fara samun tikitin.

Wannan ya biyo bayan nasarar da ta samu jiya da ci 1 – 0 akan Austria.

Wannan nasara ta sa Denmark ta kafa tarihin lashe wasannin ta guda 8 inda ta samu maki 24, ba tare da ta bari an jefa mata koda kwallo guda a ragar ta ba.

No comments