Daga Hussaini Ibrahim, Gusau A jiya Alhamis 7 ga Oktoban 2021, Rundunar 'Yan Sanda ta kai samame Dajin Tsibiri a Karamar Huk...
Daga Hussaini Ibrahim, Gusau
A jiya Alhamis 7 ga Oktoban 2021, Rundunar 'Yan Sanda ta kai samame Dajin Tsibiri a Karamar Hukumar Maradun inda suka yi nasarar ceto mutane 187 da aka sace a ƙauyen Rini dake cikin ƙaramar hukumar Bakura da ƙauyen Gora a ƙaramar hukumar Maradun da ƙauyen Sabon Birni da ke Shinkafi a ƙaramar hukumar Shinkafi.
Mutanen da aka sace wadanda suka shafe watanin da dama a hannun masu garkuwa da mutane an kubutar da su ba tare da wani sharadi ba.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara, CP Ayuba N Elkanah ya mika wadanda aka ceto ga wakilin Mai Girma Gwamna Dr Mohammed Bello Matawalle MON, ga Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Kabiru Balarabe Sardaunan Dan Isa .
Kwamishinan ya ce, sabbin matakan tsaro a Jihar na haifar da gagarumin nasara, domin hakan ya kai ga samun nasarar kubutar da mutane da dama da aka sace tuni suna cikin iyalan su.
Hakazalika, an cafke 'yan fashi da abokan aikin su, an gurfanar da wasu a gaban kotu yayin da wasu ake gudanar da bincike cikin sirri a akan su.
Kwamishinan ya ci gaba da ba da tabbacin cewa, 'Yan sanda da sauran hukumomin tsaro za su ci gaba da yin iya kokarinsu don tabbatar da dawowar dawwamammen zaman lafiya da tsaro a jihar. Ya jajantawa wadanda abin ya rutsa da su kan wahalar da suka sha yayin da suke tsare kuma ya yi alkawarin cewa 'yan sanda za su ninka kokarin su don kare rayuka da dukiyoyin' 'yan jihar Zamfara.
Wakilin Gwamna Bello Matawalle ya karbi wadanda abin ya rutsa da su, ya gode wa ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro saboda jajircewa da aiki tukuru wajen aiwatar da sabbin matakan tsaro, sannan ya ba su tabbacin gwamnatin jihar na ci gaba da ba su goyon baya da karfafa gwiwa don gudanar da ayyukansu yadda ya kamata. Ya kuma kara da cewa, gwamnatin jihar za ta tabbatar da cewa an yi wa wadanda abin ya shafa kulawa mai kyau kafin a sake saduwa da iyalansu.
Gwamnan Zamfara Bello Matawalle, a madadin wakilinsa, Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Balarabe Dan Isa, ya nuna godiyarsa ga rundunar ‘yan sanda kan yadda ta kubutar da wadannan mutane daga hannun 'yan bindigar masu tayar da kayar baya na tsawon wata da watanni.
No comments