Shugaban Sojin Nijeriya, Laftanar Janar Farouk Yahaya Daga Wakilinmu A ranar Talatar 5 ga watan Oktoban 2021 ne, gwamnatin Jihar Kaduna ta...
Shugaban Sojin Nijeriya, Laftanar Janar Farouk Yahaya |
Daga Wakilinmu
A ranar Talatar 5 ga watan Oktoban
2021 ne, gwamnatin Jihar Kaduna ta fara rusa daruruwan gidaje da sauran
gine-ginen gidaje dake Unguwar Graceland a bayan Kwalejin Fasaha ta Koyar da
Jirgin Sama (NCAT) dake Samarun Zariya kamar yadda MADOGARA ta labarto.
Wani bangare na gidajen da aka rushe a Unguwar Graceland. |
Wakilinmu da ya halarci Unguwar kafin
a kai ga rushe gidajen ya ga mazauna da yawa suna ta kuka a yayin da suke
ficewa cikin gaggawa daga gidajensu da abin da ya rage na kadarorinsu daga
baraguzan gidaje da aka rushe musu.Sai dai kafin a kai ga rushewa, wadansu
ba’adin mutanen Unguwar sun yi sa’ar samun damar kwashe wadansu kayayyakinsu
masu muhimmanci kafin hukumar raya birane ta jihar Kaduna (KASUPDA) ta kai
kayayyakinta ta fara rushe gidajen dake wurin.
Bayan jimami da kukan da ya biyo
bayan rushe muhallin, akwai kuma zargin kashe wadansu masu gidajen da ake
zargin sojoji da aka tura wurin rusa wurin sun aikata, duk da cewa rundunar
‘yan sandan jihar Kaduna ta musanta batun kashe-kashen da kuma harbin da sojoji
suka yi ba bisa ka’ida ba.
Kazalika, bayanai sun nuna cewa sama
da shekaru 10, batun mallakar fili a wurin, inda aka gina gidajen yana gaban
shari'a tsakanin al'ummomi muhallin da Kwalejin koyon tukin jirgin Sama (NCAT).
Mazaunin Unguwar ya shaidawa
majiyarmu cewa; tun ranar Asabar; “mutane da dama suka fara barin Unguwar inda
suka rika kwashe muhimman kayayyakinsu domin kaucewa lalata musu shi”, ya
tabbatar.
Wakilinmu da ya ziyarci a Unguwar da
safiyar ranar Larabar 13 ga watan Oktoban 2021, ya iske daruruwan gidaje a
rushe a bayan Kwalejin NCAT din, wanda ganau suka tabbatar mana da cewa KASUPDA
ce ta rushe su a makon da ya gabata na 5 ga Oktoban 2021.
Wasu mazauna yankin, wadanda suka yi
magana da manema labarai sun yi kira ga gwamnati "da ta nuna jinkai ta yi
la’akari da halin da muke ciki kuma ta taimaka mana", inji su.
Mazauna Unguwar sun ce sun mallaki
filin ne bisa doka tare da mallakar duk wasu takardu na doka daga gwamnati.
Sai dai lokacin da majiyarmu ta tuntubi
kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Mohammed Jalige, kan batun kashe wasu
mazauna Unguwar da ake zargin sojoji da yi a yayin Rusau din, ya ce har yanzu
bai samu rahoto ba kan zargin harbin da sojoji suka yi da kuma kashe wasu
mazauna Unguwar.
Jalige ya ce, "ba ni 'yan
mintoci kadan domin na binciki gaskiyar lamarin kuma zan dawo gare ku," in
ji Jalige. Sai dai har ya zuwa hada rahoton nan, bai bayyana gaskiyar lamarin
ba.
Kungiyar masu fafutikar kare hakkin
Dan Adam, wato Kungiyar Marubutan Hakkokin Dan Adam ta Nijeriya (HURIWA), ta yi
Allah wadai da abin da ta kira ‘kisan gilla’ da aka yi wa wasu masu gida bakwai
a Unguwar Graceland kusa da Kwalejin koyon tukin jirgin Sama dake Zariya.
Kungiyar ta kare hakkin Dan Adam, a
cikin wata sanarwa daga Shugabanta na kasa, Kwamared Emmanuel Onwubiko, da
Daraktan yada labarai na kasa, Miss Zainab Yusuf, sun ce gwamnatin jihar Kaduna
ta aikata manyan laifuka akan bil adama ta hanyar amfani da karfin soji wajen
fatattakar 'yan kasa ba bisa ka'ida ba.
HURIWA suma sun yi zargin cewa sojoji
sun kashe mutum bakwai a yayin rushe gidajen Unguwar, inda suka ce; "Muna da tabbaci cewa ya zuwa yanzu mutum
bakwai ne sojojin da suka yi rakiyar jami’an rushe-rushen gwamnatin Kaduna suka
kashe”, inji su, inda suka yi ikirarin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ne
ya ba da umarnin yin hakan domin bai wa kwalejin jirgin sama damar fadada
wuraren horas da ita a kusa da su.
Sun nuna mamakinsu bisa dokar da
shugaban kasar ya yi amfani da shi wajen “take hakkin ‘yan kasa, wasu daga
cikinsu sun yi aiki tukuru domin gina tattalin arzikin jihar Kaduna ”.
“An jawo hankalinmu ga irin
wahalar da wani Likita ya sha, wanda aka ruguza gidansa a Zariya da safiyar
jiya (Talata) inda aka yi watsi da shi bayan ya roki Gwamnatin Jihar Kaduna
cewa gidan shi ne duk abin da ya mallaka a rayuwar nan”, inji HURIWA.
Ta ci gaba da cewa; "an azabtar
da shi ta jiki, ta kwakwalwa da zuciya, kuma an rushe kadarorinsa ba tare da
la'akari da shekarunsa ba da kuma cewa ya yi ritaya a matsayin ma'aikacin
gwamnati bayan ya yi kusan shekaru 40 na rayuwarsa mai albarka”.
“Matakin da gwamnatin jihar
Kaduna ta dauka haramtacce ne, ya sabawa kundin tsarin mulki, kisan kai ne, cin
mutunci ne, abin kyama ne kuma abin zargi ne. Muna kira ga Majalisar [inkin
Duniya, Tarayyar Turai, Amnesty International, Human Rights Watch na New York
da duk mutanen da ke da niyyar yin Allah wadai da wadannan munanan laifuffukan
da Sojojin Nijeriya ke aikatawa tare da neman a yi adalci ga wadanda aka kashe
ba bisa ka’ida ba”, HURIWA ta jaddada.
Ta kuma kara da cewa; "Muna kira
da a kama tare da gurfanar da dukkan jami'an tsaro da kwamandojin Sojojin da
suka ba da umarnin kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba wanda laifinsu
kawai shi ne neman amfani da karfinsu wajen kare kadarorinsu".
Kungiyar ta jaddada cewa ta yanke
shawarar rubutawa Majalisar Dinkin Duniya, Kungiyar Tarayyar Turai da Kungiyar
Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS), domin kai karar gwamnatin
Kaduna da Gwamnatin Tarayya kan kisan gilla da aka yi wa 'yan kasa a Zariya.
No comments