Shugaban majalisar dattijan Najeriya, Ahmad Lawan ya taya al'ummar Musulmi murnar zagayowar ranar Maulidi a wata sanarwa da ya fitar. ...
Shugaban majalisar dattijan Najeriya, Ahmad Lawan ya taya al'ummar Musulmi murnar zagayowar ranar Maulidi a wata sanarwa da ya fitar.
BBC ta labarto cewa Ahmed Lawan ya ce ranar Maulidi rana
ce da ya kamata Musulmi da sauran mabiya wasu addinan su tuna da alfanun zaman
lafiya da girmama juna kamar yadda Annabi Muhammadu Salallahu Alaihi Wasallamya
koya mana tsawon rayuwarsa ta tsoron Allah.
Ya ce yin hakan na da matukar amfani
a yanzu da ake tsananin bukatar waɗannan halaye nasa don kawo waraka a ƙasarmu
tare da karfafa danƙon zumunci a matsayinmu na mutane masu imani kuma ƴan
Najeriya.
"Gwamnatin Najeriya da
Majalisar dokoki za su ci gaba da yin aiki sosai don samar da yanayi mai kyau
na zaman lafiya da fahimtar juna da ci gaba Najeriya," a cewarsa.
Ya kuma bukaci yan Najeriya su ci
gaba da addu'a da tallafa wa hukumomin tsaro a koƙarinsu na kare yan kasar.
No comments