Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Shaidar Shiga Jami'a Ta Bogi: Jami'ar MAAUN Ta Fadakar Da Al'umma Kan Ayyukan 'Yan Damfara

Hukumar gudanarwa ta Jami'ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN), ta fadakar da al'umma kan ayyukan wa...Hukumar gudanarwa ta Jami'ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN), ta fadakar da al'umma kan ayyukan wadansu 'yan damfara da suke fitarwa da kuma bayar da shaidar shiga Jami'a ta bogi ga mutanen da ba su ji ba ba su gani ba. 

Jami'ar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da shugaba kuma mu'assasin Jami'ar 'Maryam Abacha American University', Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo kuma aka rabawa manema labarai a Kano a ranar Alhamis. 

A cewar sanarwar, shawarar ta zama dole ne  la’akari da gaskiyar cewa jami’ar ba ta da wata alaka da masu damfara da abokan aikin su.

Sanarwar, duk da haka ta shawarci jama'a da ke son yin mu'amala da jami'ar, da su ziyarci mazaunin ta na dindindin da ke lamba 5, Adamu Abubakar Gwarzo, Hotoro GRA, a karamar hukumar Nassarawa a Kano ko ofishin hulɗarta da ke Kano da Kaduna ko adireshin yanar gizon ta a www.maaun.edu.ng

A cewar sanarwar, jami'ar ba za ta dauki alhakin duk wani ma'amala daga wadancan 'yan damfara ba saboda haka ka da wadanda abin ya shafa su yi tsammanin wani diyya ko maidawa daga jami'ar.

"Hukumar gudanarwar ta Jami'ar tana son sanar da Jama'a cewa ba ta fara siyar da fom ɗin shiga ba balle ta ba da shaidar shiga. Don haka, ya kamata mutane su lura.

Don haka, sanarwar ta shawarci jama'a da su yi hakuri domin jami'ar za ta sanar da kwanan watan da za a fara sayar da fom din shiga wanda zai kasance ta kafafen watsa labaran da suka dace.

Hotunan Takardun boge da 'yan damfarar ke rabawa; 


No comments