Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Sojin Nijeriya Sun Tabbatar Da Kisan al-barnawi Jagoran ISWAP

Ma’aikatar tsaron Nijeriya ta tabbatar da mutuwar jagoran kungiyar ISWAP Abu Musab al-Barnawi wanda cikin watan jiya, tun farko ...


Ma’aikatar tsaron Nijeriya ta tabbatar da mutuwar jagoran kungiyar ISWAP Abu Musab al-Barnawi wanda cikin watan jiya, tun farko jita jita ta fara sanar da mutuwar shugaban a yayin wani fadan cikin gida tsakanin mayakan kungiyar da na Boko Haram.

Wani babban Kwamandan rundunar Sojin Najeriya da ke tabbatar da mutuwar ta al-Barnawi Lucky Irabor yayin wani taron manema labarai a yau Alhamis ya ce tabbas jagoran na ISWAP ya mutu kuma babu wata tantama ga mutuwar tasa.

Janar Irabor bai fayyace ta yadda ko kuma lokacin da aka kashe al-Barnawi ba, duk da cewa wasu bayanai sun nuna yadda jagoran wanda da ne ga ma’assasin kungiyar Boko Haram wato Muhammad Yusuf ya mutu sakamakon rikici tsakanin bangarorin ta’addancin biyu.

A bangare guda ita kanta kungiyar ta ISWAP har kawo yanzu ba ta fito fili ta sanar da mutuwar jagoran na ta ba.

Tun kafin yanzu dai rundunar Sojin Najeriya a lokuta da dama ta yi ikirarin kisan al-Barnawi wanda ya fara shugabancin ISWAP tun daga shekarar 2016 lokacin da tsagin ya balle daga Boko Haram tare da fara biyayya ga babbar kungiyar ta’addanci ta duniya IS.

Tun bayan mutuwar jagoran Boko Haram Abubakar Shekau, al-Barnawi ya ci gaba da jan ragamar ayyukan ta’addanci a yankin arewa maso gabashin Nijeriya dama yankunan Tafkin Chadi, sai dai ya ci gaba da fuskantar hare-hare daga wasu ‘ya’yan kungiyar Boko Haram da suka ki mika wuya ga ISWAP.

Fiye da mutane dubu 40 hare-haren Boko Haram ya kashe a Najeriya daga 2009 zuwa yanzu yayin da mutane fiye da miliyan biyu suka rasa matsugunansu galibi a jihohin yankin na arewa maso gabas.

No comments