Daga Wakilinmu ‘Yan bindiga a karkashin jagorancin Turji, sun kai hari a babbar kasuwar garin Goronyo ta jihar Sakkwato. Ganau sun bayyana c...
Daga Wakilinmu
‘Yan bindiga a karkashin jagorancin Turji, sun
kai hari a babbar kasuwar garin Goronyo ta jihar Sakkwato.
Ganau sun bayyana cewa; ‘yan
bindigar sun zo daruruwansu, inda suka kai hari a kasuwar da da misalin karfe
4:50 na yammacin ranar Lahadi, a daidai lokacin da mutanen kauyakun ke saye da
sayarwa, wanda nan take suka bude musu wuta.
Majiyarmu ta labarto mana cewa; ‘yan
bindigar sun kwashe fiye da awa biyu ba tare da sun fuskanci wata turjiya daga
hukumomin tsaro ba sakamakon babu hanyar da za a sanar da su saboda katse
sadarwa da aka yi a yankin.
A cewar majiyarmu, akalla gawarwaki
40 aka kirga a daren ranar Lahadi.
Bayanai daga wadansu mazauna garin
na Goronyo, sun tabbatarwa da majiyarmu ta jaridar DailyStar cewa akalla ya
zuwa yanzu gawarwaki 62 aka ajiye a babban asibitin Gwamnati na Goronyo ya zuwa
safiyar yau Litinin. Banda wadanda ‘yan’uwa suka dauki gawarwakin ‘yan’uwansu
domin yi musu jana’iza.
Kuma bayanai sun tabbatar da cewa da
yawa sun bace har yanzu ba a gan su, a yayin da ake tsammaninsu wasu sun shige
daji ne sakamakon gujewa harbe-harben ‘yan bindigar.
Sannan rahotanni sun ce an jikkata
da dama wanda a halin yanzu wasu ke karbar magani a asibitin. Wasu kuma sun
samu matsalar kwakwalwa sakamakon dimaucewa daga harin ‘yan bindigar.
Ya zuwa hada rahoton nan, duk
yunkurin da muka yi domin jin ta bakin Kakakin ‘yan sandan jihar Sokoto, abin
ya ci tura.
Kasuwar Goronyo dai babbar kasuwa ce
ta albasa da shanu.
No comments