Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

YANZU-YANZU: Shaikh Zakzaky Da Matarsa ​​Sun Maka Gwamnati A Kotu Bisa Kwace Musu Fasfo

Shaikh Ibraheem Zakzaky da mai dakinsa Malama Zeenah Ibrahim, sun garzaya babbar kotun Tarayya da ke Abuja domin kalubalantar kw...


Shaikh Ibraheem Zakzaky da mai dakinsa Malama Zeenah Ibrahim, sun garzaya babbar kotun Tarayya da ke Abuja domin kalubalantar kwace musu fasfunansu na kasa da kasa da Hukumar tsaro ta DSS da kuma babban lauyan gwamnatin Tarayya suka yi.

A cikin karar da suka shigar domin tabbatar da hakkinsu mai lamba FHC/ABJ/CS/230/2021, wanda ofishin Falana ta shigar, Shaikh Zakzaky da Malama Zeenah Ibrahim sun shaida wa kotun cewa an ga fasfo din su na karshe a hannun Hukumar Leken Asiri ta Kasa (NIA) wadanda a hukumance suka musanta cewa yana hannunsu. 

Kafin wannan, Hukumomin biyu sun bayyana cewa fasfo din su ya ɓace. Sai dai a kokarin sabunta fasfunan na su a hannun Hukumar shige da fice ta kasa, an bayyana cewa hukumar DSS ta yi fashin fasfo din su. Dukkan wata dama da aka nema a wurin DSS akan su cire wannan takunkumin, amma sun kawar da kai bisa hakan. 

Sun nemi kotu da ta tilastawa wadanda ake kara su saki fasfo din a gare su, ko kuma a dauke musu 'jan fentin' takunkumin da aka kakaba musu a kan fasfo din su. Kuma a aiwatar da hakkokinsu na 'yancin walwala, da kuma bada umurni na dindindin kan dakatar da wadanda ake kara kan ƙarin ci gaba da tursasawa da kuma ci gaba da nuna halayyar tozartarwa.

Sun kuma nemi Kotun da ta umarci wadanda ake kara da su biya diyyar Naira Biliyan Biyu baki daya a matsayin misali kan abin da ya faru na take masu hakkokinsu na walwala, bada dama wajen fayyace gaskiya da kuma lalata musu kadarori.

Sun ce idan babu wani umarni daga kotu, kwace fasfunan na su da wadanda ake kara suka yi barazana ce ga rayuwarsu, tunda hakan ya hana su damar fita neman kulawar gaggawa ta lafiya a wajen kasar kamar yadda Likitocin su suka ba da shawara.

            Ga kwafin takardar karar; 

No comments