Yau talata 19 ga watan Oktoba al’ummar Musulmi a sassan Duniya ke bikin murnar zagayowar ranar 12 ga watan Rabi’ul Awwal ranar da ake dang...
Yau talata 19 ga watan Oktoba al’ummar Musulmi a sassan Duniya ke
bikin murnar zagayowar ranar 12 ga watan Rabi’ul Awwal ranar da ake dangantawa
da haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su kara
tabbata a gareshi.
Yayin bikin Mauludin dai bisa al’ada Musulmin galibi mabiya Sufaye
kan yi dafifi tare da yawaita zikiri salatin Annabi baya ga mabanbantan kasidun
yabo ga fiyayyen halitta, inda a bangare guda Iyaye kan yiwa yaransu sabbin
dinkuna yayinda mawadata kan yanka raguna da shanu baya ga girke-girken alfarma
don hidimar ranar da ake yiwa gagarumin biki.
Kalmar ta Mauludi wadda ta samo asali daga Larabci da ke nufin
‘‘haihuwa’’ a wasu yarukan na da sunaye daban kamar Havliye ko Donba ko kuma
Gani, tarihi ya nuna cewa an fara bikinta ne don tunawa da haihuwar fiyayyen
halitta Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi wa sallam tun daga shekarar 1207 a
Iraqi bisa jagorancin Muzaffar al-Din Gokburi dan uwa ga shugaban daular
Ayyubid sultan Saladin da ke jagorancin daular musulunci a wancan lokaci.
Bayan daular ta Ayyubid daular Ottaman ta taimaka wajen tabbatar da
bikin a kowacce shekara cikin kasashen musulmi, inda ranar ta 12 ga watan
Rabi’ul Awwal ke matsayin gagarumin biki har bayan gushewar daular inda bikin
yafi samun karbuwa a kasashe irin Turkiya da Masar da Iraqi da Syria da
Pakistan da India da Malaysia da Indonesia sai kuma kasashen Afrika inda
Najeriya da Senegal ke kan gaba.
Kusan dukkanin kasashen Duniya da Musulmi ke da rinjaye na gudanar
da bukukuwan na Mawludi tare da bayar da hutun ranar a kowacce shekara don
gudanar da shagulgula in banda kasashen Saudiya da Qatar wadanda ke kallon
bikin a matsayin lamarin da ba karbabbe ba a addinin Islama.
-Rfi Hausa
No comments